Fifa Ranking: France ta koma ukun farko a kan gaba a tamaula a duniya

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Mbappe

An wallafa

Faransa ta koma ta uku a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon kafa a duniya, bayan da Fifa ta fitar da jadawali ranar Alhamis.

Tawagar ta yi wannan namjin kokarin, bayan da ta lashe UEFA Nations League ranar 10 ga watan Oktoba, bayan da ta doke Sifaniya a wasan karshe a San Siro a Italiya.

Mai rike da kofin duniya tana mataki na hudu a baya kafin fitar da jadawalin da Fifa ta yi ranar Alhamis, yanzu ta koma ta uku, bayan da ta ci Belgium a wasan daf da karshe a gasar ta nahiyar Turai.

Tawagar Belgium ta ci gaba da zama ta daya a iya kwallo a duniya, sai kuma Brzail wadda ke mataki na biyu a jerin wadanda ke kan gaba a taka leda a duniya.

Bayan da Faransa ta yi sama a kan jadawalin Fifa ta rikito da Ingila daga mataki na uku zuwa ta biyar, yayin da Italiya mai rike da kofin nahiyar Turai ta koma ta hudu.

Tawagar Sifaniya ta kara yin sama da tako daya ta koma ta bakwai saman Portugal, Jamus tako biyu ta yi zuwa ta 12, yayin da New Zealand ta koma ta 111, ita kuwa Indonesia ta kara yin sama zuwa ta 165.

Ireland ta Arewa ta yi kasa sosai zuwa mataki 11 ta koma ta 58.