Hotunan Afirka na mako 15-21 Oktoban 2021: Zane da zanga-zanga da jima

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓun hotuna daga faɗin nahiyar Afirka da ma na wasu ƴan nahiyar a wasu sassan duniya.

Short presentational grey line
A man dressed in black smiles as he walks past rows of colourful paintings.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum na tafiya ta kusa da wasu zane-zanen da ake sayarwa a bakin titi a Abuja babban birnin Najeriya a ranar Litinin.
A protestor in Abuja shouts and holds a placard that reads "say no to police brutality".

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kwana biyu bayan nan mutane sun fita zanga-zanga a kan tituna don nuna ɓacin ransu kan rashin ɗaukar mataki daga hukumomi na magance cin zarafin da ƴan sanda ke yi a Najeriya, shekara ɗaya cif bayan zanga-zangar da ta karaɗe ƙasar ta Endsar.
A man works at the Chouara Tannery in Fez.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Asabar wani mutum na jimar fata a ɗaya daga cikin tsofaffin marina da ke birnin Fez na Moroko.
A model gets ready in the backstage area during the third edition of East Africa International Fashion Week in Nairobi, on October 16, 2021. - The annual fashion event created by a former Kenyan model attracts fashion enthusiasts and buyers to see six different collections by designers from Kenya, Uganda and Tanzania.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A wannan ranar kuma, wata mai tallar kayan ƙawa tana ƙwalisa a taron kayan ƙawa na ƙasa da ƙasa na Afrika...
Models talk in the backstage area during the third edition of East Africa International Fashion Week in Nairobi, on October 16, 2021. - The annual fashion event created by a former Kenyan model attracts fashion enthusiasts and buyers to see six different collections by designers from Kenya, Uganda and Tanzania.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wannan ne karo na uku da ake taron...
People watch a model on a runway at East Africa International Fashion Week.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar a wajen taron mata ƴan ƙwalisa sun nuna adonsu musamman daga Kenya da Uganda da Tanzaniya.
An Asec Mimosas supporter in yellow, black and white.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani magoyin bayan Asec Mimosas ya sanya launin tawagar, a lokacin da tawagar Ivory Coast ta fafata da ta Aljeriya a gasar zakarun Afirka ranar Asabar a Abidjan.
A blue car parks in front of pink and green houses.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A wannan ranar a Afirka Ta Kudu, wani mutum ya ajiye motarsa a Bo-Kaap a birnin Cape Town...
A bridal party walks up from the beach.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A wani wajen kusa da nan kuma an yi liyafar auren wasu ne a bakin teku a ranar Asabar din...
Runner line up ahead of the Cape Town Marathon.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Sannan a ranar Lahadi kuma, an yi gasar tsere a Cape Town.
Sudanese protesters take part in a sit-in.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar mutane sun yi zanga-zanga a Khartoum babban birnin Sudan, suna neman sojoji su karɓi iko.
1px transparent line
Musicians play during a demonstration by supporters of opposition leader Martin Fayulu, against changes to the independence of the country's electoral commission, in Kinshasa.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Asabar ma an yi ta zanga-zanga a babban birnin Jamhuriyya Dimokradiyyar Congo inda mutane ke neman a samar da hukumar zaɓe mai zaman kanta.
Ibrahim, a spear-fisherman, poses for a portrait along the coastline of Dakar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani masunci a Senegal Ibrahim yana tsaye dauke da fatsarsa a gabar teku a Dakar ranar Talata.
A woman takes a photo of Ben Enwonwu's The Court of the Oba of Benin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Asabar a London, an kafe zanen da wani dan Najeriya Ben Enwonwu ya yi a gidan gwanjon kaya na Sotheby.
Women take a selfie next to a poster.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar kuma an yi bikin nuna fina-finai na Fespaco a Burkina Faso , inda kwanaki kadan bayan nan aka kama wasu baƙi biyu suna ɗaukar hoton selfie...
An attendee wears a protective face mask with an image of Burkina Faso's former President Thomas Sankara.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Bikin nuna fina-finan ya zo daidai da ranar da aka fara sauraron ƙarar kashe tsohon shugaban ƙasar Thomas Sankara, wanda kisansa ya girgiza ƙasar a shekarar 1987. Wata mata ta satakunkumin mai ɗauke da hotonsa.
Three girls hug each other and smile.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An dauki hoton waɗannan yaran ne a birnin Lomé na Togo a ranar Laraba.
A wreath of flowers is pictured on a bridge above the Seine river.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, a birnin Paris mutane sun yi ta ajiye furanni don tunawa da ƴan ALjeriyan da ƴan sanda Faransa suka kashe hekara 60 fda suka gabata. A kalla mutum 100 aka kashe, inda wasun su aka jefa su a Kogin Seine suka nutse.

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka.