Eid El-Maulud: Wasu hotunan yadda aka yi bikin Maulidi a fadin duniya

An wallafa

Musulmi a kasashen duniya daban-daban sun gudanar da bukukuwan maulud, inda da dama suka yi tattaki da tarukan yabo ga Annabi Muhammad SAW.

Ranar 12 ga watan Rabiul Awwal ake bikin bikin Maulidi domin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad.