Maulud: Abu uku game da watan Rabiul Awwal da aka Haifi Manzon Allah

An wallafa

Rabiul Awwal, wata ne na kalandar musulunci da wani bangaren musulmin duniya ke bikin zagayowar ranar da aka haifi manzon Allah, Annabi Muhammad S.A.W.

Musulmai da dama sun yi amannar cewa a watan Rabiu'l Awwal, aka haifi Annabi Muhammadu (SAW).

Sai dai ba dukkanin Musulmi ne ke bikin haihuwar Ma'aiki SAW, saboda sabanin fahimta. Akwai wani ɓangare na malamai da ke nuna rashin dacewar gudanar da bikin maulidi.

Amma wani ɓangare na malamai na kwadaituwa da maulidi suna masu cewa al'ummar Musulmai za su iya yin dukkan abin da suke gani Allah da Manzonsa sun yarda a yi, sai su yi domin nuna murnarsu.

BBC ta tattauna da Alaramma Muhammadu Mash-hud, wani malamin darikar Tijjaniyya a Kano, dangane da watan Maulidi, Rabiul Awwal.

Muhimmancin watan Maulidi

Malamin ya ce cikin watan Rabiul Awwal ne Allah (SWA), ya yi wa halittarsa kyautar da ta fi kowacce irin kyauta daraja wato Manzon Allah SAW.

"Wata ne mai girma na haihuwar Annabi - Idan da Allah ya ga dama sai ya sa a haifi Annabi a Ramadan ko watan Aikin Hajji kuma idan Allah ya ga dama da sai Ya sa a haife shi a ranar Juma'a"

Ya ce hikima ce ta Allah, haihuwar Annabi a watan Rabiul Awwal.

Malamin ya kuma ce watan Rabiul Awwal ana nufin "kaka ta farko."

"Lokacin ne na wasu taurari guda bakwai - waɗanda suka yi daidai da Rabiul Awwal da aka haifi Annabi," in ji Alaramma Muhammadu Mash-hud.

Ya ce babu ƙaulani ko shakka cewa an haifi ne a watan Rabiul Awwal.

Fa'idojin Rabiul Awwal

Alaramma Muhammadu Mash-hud ya ce babban fa'idar watan Rabiul Awwal shi ne haihuwar annabi a cikin watan.

Kuma ya ce babu ranar murna kamar ranar haihuwar annabi - 'Babbar fa'ida shi ne murnar haihuwar Annabi."

"Annabi ne ya fi cancanta idan lokacin haihuwarsa ya zagayo a yi murna," in ji malamin.

Ya ƙara da cewa duk wani abin murna da za a yi bai kai kamar zuwan Kur'ani da zuwan Annabi ba - "ni'mar samuwar annabi ita ce babbar ni'ima da Allah ya ba mu"

Ayyukan Ibadah

Alaramma Muhammadu Mash-hud ya ce ana son idan watan ya kama, musulmi ya dage da yi wa Annabi SAW salati.

Ya ce salati ne ya fi cancanta ga masoyan Annabi duk da cewaa duk juma'a ana son a yawaita yi wa annabi salatin.

Ya ce a ranakun Alhamis ko Juma'a, "Annabi yake karkato da kunensa ya ji salatin masu salati kuma babu girman salati kamar na ranakun Alhamis da Juma'a na wannan watan da aka haifi Annabi.

Bikin Mauludi

Al'ummar Musulmai kan yi hidima a wannan lokaci, inda kamar a Najeriya musamman a jihohin arewacin ƙasar, makarantun allo ko na Islamiyya kan shirya mauludi ta hanyar ƙayata waje a gayyaci manyan baƙi a zo a bai wa ɗalibai karatu da waƙoƙi na yabon Annabi su zo su rinƙa yi.

Wata al'ada kuma za ka ga a wannan rana a kan dafa abinci da nama musamman kaji a raba gida-gida na maƙwabta kamar ranar sallah.

A wani lokaci ma har ɗinki ake yi wa yara don su sanya sabon kaya kamar sallah.

Ga wasu mutanen kuma a kan shirya taron lakca inda za a gayyato malamai su yi wa'azi.