An soke bayar da tazara a Masallacin Ka'aba da na Madina a Saudiyya

Asalin hoton, @hsharifain
An soke bayar dokar bayar da tazara da aka tilasta a Masallacin Ka'aba a Makkah da kuma na Annabi a Madina, kamar yadda hukumomin da ke kula da Masallatan Biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain suka bayyana.
Matakin zai fara aiki ne daga ranar Lahadi, inda hukumomin suka ce za a ci gaba da cika masallatan biyu kamar yadda aka saɓa kafin annobar korona.
Hukumomin masallatan biyu masu daraja Haramain Sharifain sun ce "za a ɗage bayar da tazara bayan Sallar Isha'i a ranar Asabar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Wannan kuma na zuwa bayan ma'aikatar kula da harakokin cikin gida ta bayar da umarnin buɗe masallatan gaba ɗaya da kuma sasasauta matakan kariya da aka ɗauka.
Hakan na nufin za a bari mutane su gudanar da ibadah ba wani shamaki a wuraren Dawafi da Safa da Marwa a Masallacin Ka'aba.
Sai dai tun da farko hukumomin Saudiyya sun ce dole sai wanda ya kammala allurar rigakafin korona (guda biyu) kafin shiga masallacin Makkah da Madina.
Sannan har yanzu dokar sanya abin rufe baki da hanci na nan ga baƙi masu ibadah da kuma ma'aikatan da ke kula da masallatan.
Saudiyya ta sassauta matakan korona ne bayan raguwar masu kamuwa da cutar a ƙasar.
An dakatar da yin Umrah a watan Maris din bara da rage yawan masu aikin Hajji tun ɓullar cutar korona kafin aka bude daga baya.









