Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ranar Matan Karkara ta Duniya: Ko wanne hali matan Nijar ke ciki?
Majalisar Dinkin Duniya ta kebe kowacce ranar 15 ga watan Oktoba, a matsayin ranar matan karkara ta duniya.
An kebe wannan ranar ce domin tunawa da irin gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arziƙin al'ummomi a yankunan karkara d amata ke bayarwa.
Karfafawa matan karkara gwiwa na da matukar muhimmanci wajen kawar da yunwa da talauci a tsakanin al'umma in ji tsohon skaatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ko Moon.
A shekarar 2012, ne aka kaddamar da wannan rana wadda aka sauyawa suna daga ranar manoma mata ta duniya zuwa ranar matan karkara ta duniya.
Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wani shiri a baya bayan nan na karfafa matan karkara da kuma karfafa samar da abinci.
A cikin kowacce al'umma, matan karakara na taka muhimmiyar rawa wajen binkasa tattalin arziki musamman a kasashe masu tasowa.
Ywancin matan karkara kan shiga aikin noma ta yadda za su noma abinci da kuma samar da ababan more rayuwa.
Kazalika mata na taka muhimmiyar rawa ta fannin ilimi yara, da kula da marassalafiya da kuma tsofaffi, a don haka ba su gudunmuwar da ta dace zai matukar taimaka musu.
To sai dai kuma a wasu kasashen kamar Jamhuriyar Nijar, matan na fuskantar matsaloli da dama da suka nisantar da su da ga burin Majalisar Dinkin Duniya.
Wasu daga cikin matsalolin da matan Nijar ke fuskanta sun hadar da rashin samun ruwan sha da ma wanda za suyi amfanin yau da kullum.
Wasu mata da BBC ta tattauna da su a Nijar din,sun bayyana cewa suna matukar shan wuya wajen samun ruwa don a wasu kauyukan kasar ma sai cikin dare mata kan fita neman ruwan da za su yi amfani da shi.
Baya ga karancin ruwan shan, matan Nijar din sun kuma koka da rashin asibitoci a kusa da su, wanda hakan ke jefa rayuwarsu dama ta 'ya'yansu a cikin mawuyacin yanayi.
Matan suka ce, idan suna dauke da juna biyu kafin su je asibiti suna shan wuya saboda nisan da ke da shi daga inda suke.
Suka ce a wasu lokuta idan nakuda ta taso musu ga ba bu asibiti a kusaa gida ko hanya suke haihuwa.
Matan sun bukaci gwamnatin kasar ta Nijar, da ta taimaka ta smaar da asibitoci a kauyuka saboda rage musu wahalar da suke sha.
Mata dai sune ginshiki na ci gaban kowacce al'umma, a don haka yana da matukar muhimmanci a rinka kyautata musu rayuwa a koda yaushe.