Ya kamata Buhari ya zaftare kasafin kuɗin Najeriya na 2022 - SERAP

Gabatar da kasafin kuɗi da Buhari ya yi

Asalin hoton, MUHAMMADU BUHARI FACEBOOK

An wallafa

Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta buƙaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya zaftare naira biliyan 26 daga cikin kasafin kuɗin kasar na shekara ta 2022.

Kudaden wanda gwamantinsa ta ware ne domin wasu ayyuka da ƙungiyar take gani ba su da muhimmanci sosai idan aka yi la'akari da cewa gwamnatin za ta ciyo ba shi ne domin rage giɓin kasafin kuɗin.

A yayin gabatar da kasafin kuɗin da shugaban ya yi a gaban Majalisar Dokokin Ƙasar a ranar Alhamis 7 ga watan nan na Oktoba, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kashe wannan naira biliyan 26 wurin gina ɓangaren kula da lafiya na shugaban ƙasa, da tafiye-tafiye na cikin gida da na waje, da harkar abinci da liyafa, da alawus na zaman taro tare da na walwala da jin daɗi.

Ganin cewa ƙasar tana ta ciyo bashi ya sa ƙungiyar ta SERAP, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar 9 ga watan Oktoba ta nemi shugaban na Najeriya da ya yanke wannan kuɗi domin rage yawan bashin da ƙasar za ta ci wajen rage giɓin kasafin kuɗin.

Kuma gwamnatin ta yi amfani da wasu daga cikin kuɗaɗen da za a samu daga yankewar wajen inganta asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya a faɗin ƙasar.

A dangane da hakan ne ƙungiyar ta buƙaci Shugaba Buharin da ya aika wa da Majalisar Dokokin Ƙasar ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi na wannan ragi da ta ce ya kamata ya yi domin samun amincewar Majalisar.

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Presidency

A sanarwar, SERAP ta ce zai zama abin ban mamaki da takaici ga ƴan Najeriya da dama su ga cewa gwamnati na kashe maƙuɗan kuɗaɗe a da yawa daga cikin waɗannan abubuwa yayin da take ta ciyo bashi, saboda haka ya kamata a yi amfani da kuɗaɗen wajen bunƙasa muhimman ayyuka da kayayyaki da ƴan ƙasar ke amfani da su.

Ƙungiyar ta ce yawan cin bashi akai-akai da gwamnati ke yi ba abu ne mai ɗorewa ba kuma ba adalci ba ne ga al'ummar Najeriya.

Ta ankarar da shugaban na Najeriya da cewa gwmnatinsa tana da alhakin tabbatar da kare buƙatu da kuma cigaban Najeriya da ƴan ƙasar.

Ta ƙara da cewa ƙarin giɓin da ke samu a kasafin kuɗi da kuma katutun bashin da ƙasar ke ɗauka na barazana ga damar ƙasar ta samun muhimman abubun jin daɗin jama'a da ayyuka, kuma hakan zai cutar da al'ummar ƙasar ta gaba, muddin ba a gaggauta ɗukar mataki a kai ba.

Ƙungiyar mai yaƙi da almundahana a takardar tata ta kuma yi kira ga gwamnatin Muhammadu Buharin da ta wallafa cikakken bayani na kuɗaɗen da ta kashe a kan aiki da kuma gyaran sashen shugaban ƙasa na asibitin fadar gwamnatin da na kujeru da tebura da makamantansu tun daga wata Mayu na 2015.

Abin damuwa

Wani abun da shi ma ake nuna damuwa a kansa game da kasafin ƙudin na Najeriya na shekara mai zuwa shi ne yadda gwamnatin ta ware naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari shida domin sayen motoci da sauran abubuwan da suka dangance su, saɓanin naira miliyan 436 da aka ware a 2021 a kan hakan.

Gwamnatin ta ware sama da naira miliyan 180, domin sayen tayoyin mota da motoci masu silke, da marassa silke da sauran nau'ukan motoci, saɓanin naira miliyan 16,194,297 da gwamnatin ta ware a kan waɗannan kayayyakin a shekarar da ta wuce.

Kasafin Kudina taƙaice:

  • A kasafin na 2022, wanda ya haura naira tiriliyan 16, shugaban ya ce zai mayar da hankali wajen kammala ayyukan da gwamnatinsa ta fara
  • Gwamnatinsa za ta ciyo ƙarin bashi har kimanin naira tiriliyan shida, don cike giɓin da za a samu
  • An yi kasafin kuɗin ne a kan farashin gangar ɗanyen mai ɗaya a kan dala hamsin da bakwai, da ƙiyasin hako ganga 1.88 a kowce rana.