Waiwaye: Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya daga 3 zuwa 9 ga watan Oktoba

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY
Makon farko na Oktoba ya ƙare har an shiga wani sabo. Abubuwa da dama sun wakana amma za mu duba muhimmai daga cikin abubuwan da suka faru a makon da muke bankwana da shi.
Buhari ya gabatar da kasafin kuɗi na 2022
Ranar Alhamis 7 ga watan Oktoba ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da ƙudurin kasafin kuɗin shekarar 2022 a gaban zaman haɗin gwiwa na 'yan majalisun tarayyar ƙasar.
Shugaban ya ce kasafin na shekarar 2022, zai mayar da hankali ne wajen kammala ayyukan da gwamnatinsa ta soma kuma ƙudurin kasafin kuɗin na 2022, wanda ya kai naira tirliyan 16 da ɗigo 39.
Kuɗin dai, ƙari ne a kan naira tiriliyan 13.98 na kasafin kuɗin shekara 2021.
Gwamnatin shugaban kasar ta bayyana shirinta na ciyo ƙarin bashi don samun ƙarin kudi har Naira tiliyan 6 da biliyan 258, da zata cike giɓin da za a samu a kasafin kuɗin da shugaban zai gabatar na shekarar 2022.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan ya ce majalisar dokoki za ta amince da kasafin kudin 2022 kafin karshen wannan shekarar.
Daukewar shafukan Facebook da Instagram da Whatsapp

Asalin hoton, Getty Images
Shafukan sada zumunta da muhawara na Facebook da WhatsApp da Instagram sun daina aiki tsawon kusan sa'a shida.
Kamfanin ya dora alhakin matsalar a kan wata tangarda daga wurinsu.
An kasa samun dukkanin shafukan uku mallakin Facebook a kan wayoyin hannu da intanet.
Lamarin ya shafi Najeriya da sauran kasahen duniya.
Amma Najeriyar mutane sun fara farga da abin da ke faruwa ne da misalin karfe biyar na yammacin ranar Litinin.
Gwamnonin kudu maso gabas sun ɗauki matakai kan IPOB

Asalin hoton, OTHERS
Shugabannin Kudu maso gabashin Najeriya sun yi Allah wadai da zaman gida da ƙungiyar IPOB da ke neman ɓallewa daga Najeriya ta tilastawa al'ummar yankin duk ranar Litinin.
A sanarwar da suka fitar, bayan kammala taron shugabannin yankin da suka ƙunshi gwamnonin kudu maso gabas da sarakunan gargajiya da shugabannin addini a Enugu a ranar Talata sun kuma yi Allah wadai da kashe-kashen da ake yi yankin.
Shugabannin sun ɗauki matakin ne yayin da umurnin da ƙungiyar IPOB ta tilasta wa al'ummar yankin na zaman gida ya gurgunta ayyukan kasuwanci a yankin.
Cikin matakan da suka ɗauka akwai:
- Ƙaddamar da rundunar tsaron yankin ta Ebubeagu a dukkanin jihohin kudu maso gabas kafin ƙarshen 2021
- Sun amince su bayar da goyon baya a zaɓen gwamnan Anambra da kuma yin aiki da jami'an tsaro domin tabbatar da an yi zaɓen cikin kwanciyar hankali
- Sun ɗora wa sarakunan gargajiya da shugabannin addini da suka haɗa da ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya su ci gaba da tattaunawa da matasan yankin
Zagayowar ranar da aka fara zanga-zangar EndSars
Ranar 8 ga watan Oktoba ne aka cika shekara ɗaya dai-dai da fara jerin zanga-zangar #Endsars don nuna ƙin jinin cin zarafin da ƴan sanda ke yi wa matasa a Najeriya.
An gudanar da zanga-zangar ne a shekarar da ta gabata bayan kwashe tsawon shekaru ana gangamin a shafukan sada zumunta musamman a Twitter.
Dubban daruruwan matasan Najeriya ne suka mamaye muhimman tituna don yin zanga-zangar nuna ƙin jinin mugunta, cin zarafi, da kisa ba tare da gurfanarwa a gaban kotu ba da jami'an 'yan sanda ke yi, bayan da wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta.
Bidiyon na nuna yadda jami'an 'yan sandan rundunar musamman ta yaki da fashi da makami (Sars) suka kashe wani mutum, wanda ya haifar da zanga-zangar da aka yi wa lakabi da #EndSars.
Zanga-zangar ta kara girma inda ta bazu a kasar da ma wasu manyan biranen duniya har na tsawon makonnin biyu - kuma ta saka gwamnati amincewa da rushe rundunar 'yan sanda ta musamman ta Sars, tare da kafa kwamitin gudanar da bincike kan zargin mugunta da cin zarafi da ake yi wa jami'an a fadin kasar.
Kuɓutar da mutane 180 daga hannun ƴan bindiga a Zamfara

Asalin hoton, Nuhu Dansadau
Ranar 7 ga watan Oktoba ne rundunar 'yan sanda jihar Zamfara ta sanar da ceto sama da mutum 180 wadanda 'yan fashin daji suka sace a kauyukansu.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Mohammed Shehu, ya fitar ya ce mutanen sun shafe makonni a hannun 'yan fashin dajin.
An yi nasarar ceto mutanen ne bayan wani aikin nema da ceto da jami'an tsaro suka yi a dajin Tsibiri da ke karamar hukumar Maradun a jihar ta Zamfara.
Gwamnatin jihar ta Zamfara ta ce an same mutanen cikin yanayi na galabaita sosai, domin da yawa daga cikinsu an same su da ƙuraje a jikinsu saboda cizon sauro da makamantansu.
Kotu ta yanke wa Faisal Maina hukuncin ɗauri shekara 24

A makon da ya gabata ne wata babbar kotun tarayya a babban birnin Najeriya Abuja ta yanke wa Faisal, ɗan Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar sauye-sauye ta fansho hukuncin ɗaurin shekara 24 a gidan yari.
Mai Shari'a Okon Abang ya samu Faisal da laifuka uku da suka haɗa da halatta kuɗin haram, wanda hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati EFCC ra tuhume shi da su.
Mai Shari'a Abang ya ce EFCC ta gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa Faisal ya yi amfani da wani asusun ajiya na banki na jabu a bankin UBA, inda ta can ne mahaifinsa Maina ya yi zambar kuɗi har naira miliyan 58.1.
Kotun ta ce an tura kuɗin ne asusun mai ɗauke da sunan Alhaji Faisal Farm 2, kuma Faisal da mahifinsa sun cire kuɗaɗen daga tsakanin Oktoban 2013 zuwa Yunin 2019.
Mai shari'ar ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 14 ne kan laifuka biyu sai kuma shekara goma kan laifuka biyu.
Faisal bai halarci zaman kotun ba, ana zargin ya tsere daga ƙasar tun tuni.











