Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Kane, Grealish, Rodriguez, Traore, Romero, Zouma, Milenkovic, Lookman

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester City za ta hakura da neman dan gaban Tottenham Harry Kane, mai shekara 27, idan har ta sayi abokin wasansa a tawagar Ingila, Jack Grealish mai shekara 25, daga Aston Villa. (Jaridar Manchester Evening News)

An yi wa kyaftin din na Aston Villa, Jack Grealish farashi fam miliyan 100

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An yi wa kyaftin din na Aston Villa, Jack Grealish farashi fam miliyan 100

An gaya wa gwanin dan wasan Colombia James Rodriguez, mai shekara 30, cewa ba ya cikin tsarin sabon kociyan Everton Rafael Benitez, saboda haka yana da damar tafiya idan aka samu mai sayensa a farashin da ya dace. (Jaridar Liverpool Echo)

Sau biyu James Rodriguez ya dauki kofin Zakarun Turai a Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sau biyu James Rodriguez ya dauki kofin Zakarun Turai a Real Madrid

Atletico Madrid ta sha gaban Arsenal a gogayyar sayen dan gaban Inter Milan, dan Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 23, wanda aka yi wa farashi euro miliyan 90 (fam miliyan 76.8). (Tuttosport)

Kungiyar Atalanta ta amince da tayin fam miliyan 43 da Tottenham ta yi wa dan bayanta Cristian Romero, dan Argentina mai shekara 23. (Talksport)

Leeds na sha'awar sayen dan wasan gaba na gefe na Wolves Adama Troare mai shekara 25. Dan Sifaniyar da aka yi wa farashi fam miliyan 30. (Goal)

Ita ma kungiyar Tottenham, wadda tsohon kociyan Wolves Nuno Espirito Santo, ya taba horarwa na duba yuwuwar sayen Traore. (Jaridar Mail)

Adama Traore

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tottenham ma na sha'awar sayen Adama Traore

Har yanzu West Ham na tattaunawa da Chelsea a kan dan baya Kurt Zouma mai shekara 26, inda suke kokarin cimma matsaya a cinikin. Amma kuma idan cinikin bai tabbata ba, tana shirin sayen Nikola Milenkovic dan kasar Serbia, daga Fiorentina a madadin dan Faransar. (Sky Sports)

Crystal Palace na son daukar aron dan wasan gaba, Ademola Lookman, daga RB Leipzig amma kuma da yuwuwar za ta fuskanci gogayya daga Burnley da Watford a kan dan Ingilar mai shekara 23. (Jaridar Sun)

Ademola Lookman ya tafi RB Leipzig daga Everton ne

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ademola Lookman ya tafi RB Leipzig daga Everton ne

Wakilin dan bayan Tottenham Davinson Sanchez mai shekara 25, dan Colombia, ya tattauna da Sevilla, inda ake ganin kungiyar na son maye gurbin dan wasan Faransa Jules Kounde, mai shekara 22, wanda ake dangantawa da tafiya Chelsea. (Caracol Radio daga jaridar Mail)

Wolves ta nuna sha'awarta ta sayen dan wasan tsakiya na Wales Aaron Ramsey daga Juventus, ko da yake ana ganin dan wasan mai shekara 30 ba ya sha'awar tafiya Wolves din. (Calciomercato)

Aaron Ramsey

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Aaron Ramsey

An yi wa Barcelona tayin dan gaban Wolves Rafa Mir, dan Sifaniya, wanda sau hudu kawai dan wasan mai shekara 24 ya taka wa kungiyar leda tun lokacin da ya koma can daga Valencia a 2018, kuma sau uku ana bayar da aronsa. (Sport)

Sheffield United na sha'awar karbar aron dan wasan tsakiya na Manchester United James Garner, dan Ingila mai shekara 20. (Jaridar Sun)

Burnley da Watford na kankankan a fafutukar sayen dan bayan kungiyar Hibernian, dan Scotland Josh Doig, mai shekara 19, wanda aka yi wa farashi fam miliyan 4. (Mail)

Southampton na neman fam miliyan 6 a kan dan wasan gaba dan Ireland Michael Obafemi, mai shekara 21,wanda ke daukar hankalin Blackburn. (Jaridar Sun)