Rasha za ta ɗauki shirin fim a sararin samaniya a karon farko

The hatch was eventually opened and Peresild and her fellow crew members entered the ISS

Asalin hoton, Roscosmos

Bayanan hoto, Peresild ta samu shiga kumbon sararin samaniyar
An wallafa

Rasha ta zama kan gaba a gogayyar da ake yi ta zuwa sararin samaniya da wani sabon salo, inda ta tura ma'aikatan fim zuwa tashar sararin samaniya ta kasa da kasa.

NASA na shirye-shiryen ƙaddamar da wani shiri don ɗaukar fim a sararin samaniya, wanda Tom Cruise zai fito a ciki.

A cikin fim ɗin na Rasha, wanda Klim Shipenko ya jagoranta, ƴar fim Yulia Peresild za ta taka muhimmiyar rawa.

Jirgin sama jannati samfurin Soyuz MS-19 da ke ɗauke da su ya tashi ne daga Kazakhstan, kuma cikin sa'o'i uku ya isa tashar sararin samaniya ta ƙasa da ƙasa.

Fuskar kyamarar ta mayar da hankali kan Peresild da 'yarta Anna mai shekaru 12, wacce ke kallon mahaifiyarta daga nesa cikin aminci, yayin harba jirgin sama jannatin zuwa sararin samaniya.

Matar daraktan fim ɗin, ƴar fim Sofia Karbonina, ta nuna cewa dole darakta Shipenko ya rage nauyinsa da kilo 15 kafin ya fara aikin ɗaukar fim ɗin.

Actress Yulia Peresild, cosmonaut Anton Shkaplerov and film director Klim Shipenko, wave as they attend the send-off ceremony

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Tawagar ta isa lafiya

Jirgin sama jannatin, ƙarkashin jagorancin ɗan sama jannati Anton Shkaplerov, ya tashi ranar Talata da karfe 8:55 agogon GMT. "Tawagar cikin jirgin na cikin aminci," a cewar kwamandan tafiyar, ya fada jim kadan bayan tashinsu.

Jirgin na Soyuz ya tsaya a tashar sararin samaniya ta ƙasa da ƙasa bayan sa'o'i uku kacal.

Daraktan da 'yar wasan kwaikwayon za su shafe kwanaki 12 ne kacal don ɗaukar fim ɗin a sararin samaniya.

Peresild za ta taka rawar likitar tiyatar zuciya, wadda aka tura zuwa sararin samaniya don ceton rayuwar wani ɗan sama jannati.

Automatic docking of the Soyuz was unsuccessful

Asalin hoton, Roscosmos

Bayanan hoto, An yi nasarar harba jirgin da ke ɗauke da ƴan fim ɗn

An ba da rahoton cewa wasu ƴan sama jannati biyu Oleg Novitsky da Pyotr Dubrov, za su taka rawa a fim din.

Za a gudanar da hotunan yin fim a sashin Rasha a cikin tashar. Batun ɗaukar fim ɗin a sararin samaniya ya jawo ce-ce-ku-ce a Rasha.

The hatch was eventually opened and Peresild and her fellow crew members entered the ISS

Asalin hoton, Roscosmos

Bayanan hoto, Peresild ta samu shiga kumbon sararin samaniyar

Shugaban hukumar sararin samaniya ta Rasha "Roskosmos" ne ya kawo tunanin ɗaukar fim ɗin a sararin samaniya, wanda har akwai wani lokaci da ya kori babban jami'i na hukumar, saboda wata taƙaddama da ta taso kan fim ɗin.

Sergei Krikalev, wani tsohon ɗan sama jannati, ya koma bakin aiki kwanaki kaɗan bayan yaɗa jita-jitar cewa an kore shi daga aiki.

Cosmonaut Mikhail Kornyenko ya shaida wa BBC cewa yana daya daga cikin mutane da yawa da ke adawa da aikin.

Ya ce tashar sararin samaniya ta duniya "babban wajen gwaje -gwaje ne, kuma bai kamata a kawo duk wani abu da zai shiga cikin aikin ƙwararru da ake gudanarwa a can ba."

Tashar Channel One ta Rasha ce ke ɗaukar nauyin shirya fim ɗin, kuma wani reshe na Roscosmos ya sanar da cewa aikin ba zai buƙaci kudi daga kasafin gwamnatin tarayyar Rasha ba.

Hukumar sararin samaniya ta Rasha ta shafe shekaru tana cikin matsala, saboda cin hanci da rashawa da ya mamaye tsarin kafa sansanin sararin samaniya a Gabas Mai Nisa.

Rasha ta yi barazanar ficewa daga Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Kasa da Kasa cikin shekaru hudu, saboda kayan aikin da ba su da amfani a cikin jirgin.