Yaƙin Ethiopia da Tigray: Yadda yaƙi ya rarraba kan Kiristoci a Ethiopia

Asalin hoton, Awi Communication
- Marubuci, Daga Fasikaw Menberu da Farouk Chothia
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilan BBC
- An wallafa
Wani ma'abocin ibadar Kirista, wanda a baya ba ya iya ɗaukar komai sai alamar gicciye (kuros) da littafi mai tsarki na Bible, yanzu ya duƙufa wurin ɗaukar bindiga domin yaƙar 'yan tawayen Tigray a yaƙin da ke rarraba kan ƙasar da kuma mabiya addinin Kirista.
"Ina fafata yaƙi ne da duka biyun - addu'a da kuma bindiga," a cewar Father Gebremariam Aderaw.
Ma'abocin ibadar wanda sunansa yake nufin "hadimin Mary (Maryam mahaifiyar Annabi Isa)", ya saka hannu don shiga rundunar sojan gwamnatin Ethiopia 'yan makonni bayan Firaminista Abiy Ahmed ya yi kira ga dukkan mazaje su shiga yaƙin da ake yi da 'yan tawayen Tigray People's Liberation Front (TPLF).
Ƙungiyar ta ƙaddamar da yaƙin ne a watan Nuwamba a yankinta na Tigray bayan sun samu rashin jituwa da Mista Abiy Ahmed game da sauye-sauyensa na siyasa.
"Lokacin da na lura ƙasar na ɓalɓalcewa...kuma ana kashe malaman Kirista, sai na shiga soja ina mai imanin cewa shiga yaƙin abu ne mai muhimmanci," kamar yadda Gebremariam ya faɗa wa BBC Amharic.
Ya ce tuni ya samu horon soja daga wata ƙungiya a yankin Amhara mai makotaka.
"Ba na jin tsoron jin rauni ko mutuwa a lokacin yaƙin. A shirye nake na karɓi dukkansu. Allah kaɗai nake jin tsoro," in ji shi.

"Akwai masu wa'azi fiye da 700 a Lalibela amma yanzu suna cikin ƙunci saboda ba a gudanar da wasu ayyuka saboda TPLF na iko da yankin, sannan kuma ba a biyan su albashi," a cewar Menychle Meseret, wani malamin Jami'ar Gondar da ke Amhara.
Kwanson harsasai a coci
Duk da cewa babu rahoton lalata gine-gine a Lalibela, Menychle ya ce an sace kuɗaɗe masu yawa daga coci-cocin yankin, da kuɗi da abinci da kuma wasu litattafai masu tsarki - abin da ke nuna yadda TPLF "ta ƙaddamar da cikakken yaƙi ba tare da bai wa wuraren ibada da al'adu kariya ba".
Wata kafar yaɗa labarai ta ruwaito cewa an lalata cocin Century Church of Checheho Medhanialem bayan dakarun TPLF sun kai mata hari.
Kazalika kamfanin labarai na Associated Press ya ruwaito yadda wakilinsa ya ga kwanson harsasai a cikin wata coci da aka lalata a ƙauyen Chenna Teklehaymanot.
Mazauna garin sun ce an kashe malaman Kirista shida daga cikin mutum gommai da aka kashe yayin wani hari da ƙungiyar ta kai a watan Agusta.
Dukkanin ɓangarorin sun musanta aikata laifukan yaƙi.
Kiristoci masu bin koyarwar gargajiya, su ne kashi 43 na yawan al'ummar Ethiopia, abin da ya sa suka zama rukunin mutanen da suka fi kowanne tasiri a ƙasar. Kuma yaƙin ya rarraba kan mutane da dama a yankin.

Asalin hoton, Getty Images
Firaminista Abiy 'ya yi watsi da tsarin raba addini da siyasa'
Getachew Assefa, wani malamin jami'a ne a Canada kuma mamba a wata coci da ke arewacin AMurka, ya fada wa BBC cewa yana kallon yaƙin a matsayin hanyar "karya" 'yan Tigray da kuma ƙoƙarin tilasta musu don su durƙusa wa Mista Abiy da kuma abokinsa na Eritrea, Shugaba Isaias Afwerki.
An zargi dakarun Eritrea da sace kayayyaki daga Cocin Century Debre Damo Monastery da aka gina tun a ƙarni na shida a kan duwatsun Tigray.

Asalin hoton, Getty Images
Mista Menychle ya zargi TPLF da haddasa rikicin, yana mai cewa tana yaɗa ƙiyayya a kodayaushe da kuma kalaman rarraba kan al'umma.
Shi kuwa Farfesa Getachew yana ganin tattaunawa ce kaɗai za ta kawo ƙarshen yaƙin tsakanin gwamnati da TPLF.
"Alamar gicciye da muke sakawa a jikin kayanmu da kuma fatarmu ba muna yi ne domin ado ba kawai. Idan dai har ma'anarsa na nufin zaman lafiya ne da kuma sasantawa, wajibi ne mu ci gaba da neman zaman lafiya a tsakaninmu da kuma Allah," a cewar Abune Matthias yayin wani taron addini.
Sai dai kuma Father Gebremariam ya dage kan ci gaba da yaƙi, inda yake son yin galaba kan TPLF.
"Ya zuwa yanzu mun jarraba yin addu'a, yanzu kuma za mu yi nasara da harsashi. Sai mun kawo ƙarshen maƙiyan Ethiopia," in ji shi.

Asalin hoton, AFP





