Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Wakilin Pogba ya yi magana da Madrid, Benzema na kokarin yafuto Mbappe
Manchester City na ganin cewa ta fi abokan hamayyarta Liverpool da Manchester United da Chelsea da Bayern Munich ƙwarin gwiwa wajen sayen ɗan wasan gaban Benfica Darwin Nunez mai shekara 22 ɗan asalin Uruguay. (Star)
Ɗan wasan gaban Leeds da Ingila, Kalvin Phillips na kwaɗayin sake sa hannu a sabon kwantiragi a kulob ɗin nasa. Ɗan wasan mai shekara 25 na da sauran shekara biyu a yarjejeniyar da ya saka wa hannu. (Athletic - subscription required)
Akwai yiwuwar ɗan wasan gaban Manchester kuma ɗan ƙasar Uruguay mai shekara 34, Cavani, zai iya komawa Real Madrid a tsakiyar Janairu mai zuwa sakamakon komawar Cristiano Ronaldo Old Trafford. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Manchester United na son ta yanke hukunci kan makomar ɗan wasan gaban Faransa Paul Pogba zuwa Kirisimeti. (Sun)
Wakilin Pogba ɗin Mino Raiola, ya ba Real Madrid damar ta sayi ɗan wasan mai shekara 28 zuwa kaka mai zuwa. (Express)
Bayern Munich na gab da amincewa da sabuwar kwantiragin ɗan wasan gaban Jamus ɗin nan mai shekara 26, Serge Gnabry. (Fabrizio Romano on Twitter)
Rahotanni na cewa ita ma ƙungiyar Paris St-Germain ta shiga rububin neman ɗan wasan gaban Borussia Dortmund ɗin nan Erling Braut Haaland a kaka mai zuwa. (Mirror)
Ɗan wasan tsakiyan Cagliari, Nahitan Nandez mai shekara 25 ya shirya barin kulob dinsa kamar yadda wakilinsa ya bayyana. Ɗan wasan na Uruguay na daga cikin ƴan wasan da Tottenham da Leeds da Napoli ke nema. (Calcio Napoli 24 - in Italian)
Steve Bruce zai ci gaba da zama a matsayin kociyan Newcastle ganin cewa burin mai kulob ɗin a yanzu wato Mike Ashley shi ne samun mai sayen kulob ɗin. (Sun)
Ɗan wasan gaban Faransa Karim Benzama mai shekara 33 ya ce yana da tabbacin cewa ɗan ƙasarsa ɗan wasan gaban Paris St-Germain, Kylian Mbappe, mai shekara 22 zai bi shi Real Madrid wata rana. (L'Equipe via Sun)
West Ham da Everton da Arsenal duk na kwaɗayin sayen ɗan wasan gaban Real Betis, Nabil Fekir sai dai har yanzu Betis na son riƙe ɗan wasanta mai shekara 28 ɗan Faransa. (Fichajes - in Spanish).
Real Madrid na tunanin sayen ɗan wasan gaban Leicester kuma ɗan ƙasar Belgium Youri Tielemans, sai dai komawar ɗan wasan mai shekara 24 kulob ɗin za ta iya zama alama ta tafiyar ɗan wasan tsakiyar Brazil Casemiro mai shekara 29 zuwa Paris St-Germain. (El Nacional)
Akwai yiwuwar Barcelona za ta sayi ɗan wasan gaban Manchester United Raheem Sterling domin ɗan wasan na Ingila mai shekara 26 ya buga La Liga a sabuwar shekara. (OnzeTV on Twitter)