Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zamfara: Nasarorin da ƴan sanda suka ce sun samu bayan rufe layukan waya
Rundunar ƴan sanda ta jihar Zamfara a Najeriya ta ce ta samu ɗimbin nasarori a zazzafan yaƙin da take yi da ƴan bindiga a jihar, bayan sabbin matakan tsaron da Gwamna Dokta Bello Matawalle ya ɗauka a jihar.
Rundunar ta ce jami'anta da sauran jami'an tsaro kamar sojoji da jami'an tsaron farin kaya da na farar hula sun ƙaddamar da hare-hare kan wuraren da aka san ƴan bindigar na rayuwa, don tabbatar da cewa an raba jihar da ayyukan ƴan bindigar masu taurin kai.
A wani taron manema labarai, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar SP Mohammed Shehu ANIPR wanda ya wakilci kwamishinan ƴan sanda na jihar CP Ayuba N. Elkanah, ya bayyana cewa jajircewar jami'an tsaron ta haifar da gagarumar nasara.
Ya kuma ce dalilin haka, hare-hare da kashe-kashe da satar mutane don kuɗin fansa sun yi matuƙar raguwa.
Sannan ya ce matakan da gwamnan jihar ya ɗauka sun taimaka sosai wajen hana ƴan bindigar samun abinci da man fetur da miyagun ƙwayoyin da suke sha.
Haka kuma, yanzu iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su sun daina biyan kuɗin fansa saboda tabbatar da amfani da dokokin tsaron, inda tattaunawa tsakanin masu satar mutanen da ƴan uwan waɗanda aka yi garkuwa da su ba ta yiwuwa.
Rundunar ta ce saboda haka, mutanen da ƴan bindigar ke tsare da su sun zamar masu ƙarfen ƙafa kuma ba sa iya ciyar da su don haka sun fara sako su ba tare da buƙatar kuɗi ba, bayan bincike mai zurfi da ayyukan ceto da jami'an tsaron suke yi.
Rundunar ƴan sandan ta jihar Zamfara ta ce dalilin sabbin matakan tsaron, sauran manyan laifuka da ake aikatawa a jihar kamar fashi da makami da ƙwace mota da sata da dai sauransu sun ragu sosai.
Rundunar ta ƴan sanda ta ce ta kama gawurtattun ƴan bindiga 21 a wurare daban-daban na jihar sannan sun kashe wasu guda biyar.
Haka kuma, ta daƙile hare-hare huɗu tare da kuɓuto da mutane sama da 200 da ke hannun ƴan bindiga a wurare da dama kuma tuni suka koma wurin danginsu.
Haka kuma, ta ce ƙauyuka da yankunan da a baya suke fuskantar barazanar ƴan bindiga a yanzu sun samu kwanciyar hankali inda masu bai wa ƴan bindigar bayanai ba sa iya yin haka a yanzu. Asali ma, rundunar ta kama wasu masu kai wa ƴan fashin daji bayanai da dama kuma tuni aka yanke masu hukunci bayan gurfanar da su a gaban kotu.
SP Mohammed Shehu ANIPR ya ce baya ga waɗannan nasarorin da jami'an tsaro suka samu a jihar ta Zamfara, ta kama wasu mutane mafi yawansu masu haɗa baki da ƴan bindiga ne a ƙananan hukumomin Zurmi da Shinkafi da Tsafe da hanyar Bungudu zuwa Gusau da wasu dazuzzuka a jihar.
An kama mutanen, waɗanda suka ƙunshi maza da mata, da laifuka daban-daban da suka shafi kai wa ƴan bindiga kayan abinci da makamai da taba sigari da tukwane da kwanuka da makamashi kamar man fetur da dizel da dai sauran abubuwan amfani na yau da kullum.
Sannan an kama wasu da magungunan da suka haɗa da na hana raɗaɗi kamar Panadol da na zazzaɓin cizon sauro da ruwan marar lafiya na sha da na sawa ta jijiya da sirinji da omon wanki da sukari.
Ya ce a a ƙauyen Magarya a ƙaramar hukumar Zurmi, an kama wasu da ake zargi da kasancewa ƴan bindiga inda aka kama sun a lokacin da suke fitowa daga wani wuri da ƴn bindigar ke sansani.
Bayan kama su, ɗaya daga cikinsu mai suna Abdullahi Mohammed ya bayyana cewa wani shugaban ƴan bindiga da ke ɓoye a dajin Ƴar Galadima a masarautar Ɗansadau ne ya yi hayarsa tun daga jihar Adamawa.
A cikin watan Satumban da ya gabata ne gwamnatin jihar Zamafara ta sanar da rufe layukan waya da intanet a jihar na wani ɗan lokaci a wani mataki na daƙile ayyukan ƴan bindigar da suka addabi jihar tsawon shekaru.
Ɓangarori da dama na ƙasar sun yaba wannan matakin, bayan da jihar ta Zamfara ta bayyana cewa tana kyautata zaton cewa rufe layukan waya da na intanet a jihar zai taimaka sosai wajen hana ƴan bindiga aiwatar da ayyukansu kamar yadda suka saba.
Jihar Zamafara na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar satar mutane don kuɗin fansa da fashin daji. Kusan a iya cewa ma matsalar ta fara yin ƙarfi ne a jihar kafin ta ɓulla a wasu jihohin.
Haka kuma bayan da jihar ta ɗauki wannan matakin, wasu jihohi sun bi sahunta kamar jihar Sokoto da Kaduna da Katsina.
Hukumomin tsaro da dama na ƙasar ne suka haɗa kai don gudanar da ayyukan da za su fatattaki masu aikata laifin na jihar Zamfara da ma sauran yankunan arewa maso yammacin Najeriya.
A baya an sha ɗaukar matakai da dama a jihar Zamfara kamar amfani da jiragen yaƙi da kai samame dazukan da ƴan bindigar ke rayuwa da sauransu.
Sai dai wannan ne karon farko da aka ɗauki irin wannan tsattsauran matakin a jihar mai fama da tsananin matsalar satar mutane don kuɗin fansa da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.