Shin ƙungiyar Ahlu Sunnah ta Somaliya ta dawo da ƙarfinta ne?

An wallafa

Ƙungiyar mayaƙan sa kai mai matsakaicin ra'ayi ta Ahlu Sunna Wal Jama'a, ta ƙwace iko da wata babbar jihar gwamnati ta Galmudug da ke yankin tsakiyar Somaliya.

The Sufi group engaged in fighting with the Galmudug state forces before seizing Guri'el, according to the local website Goobjoog News.

Ƙungiyar ta mabiya dariƙun Sufaye sun yi faɗa da dakarun jihar Galmudug kafin ƙwace iko da Guri'el, a cewar kafar yaɗa labaran Goobjoog.

Rahotanni sun ce fiye da mutum goma ne suka mutu.

A cikin makwannin da suka wuce ƙungiyar ta Sufaye ta yi ta haɗo kan mayaƙa da nufin ƙwace iko da garuruwan da ke ƙarƙashin ikon gwamnatin Galmudug.

Rahotanni sun ce jagororin ƙungiyar na samun goyon bayan al'ummar yankin.

Har yanzu hukumomi ba su ce komai ba a kan rikicin da kuma ƙwace iko da garin.

Ƙungiyar Ahlu Sunna Wal Jama'a wacce a baya ƙawar gwamnatin ce, an taɓa fatattakarta daga yankunan tsakiyar Somaliya a watan Fabrairun 2020, lokacin da suka yi artabu da dakarun gwamnati.

Ƙungiyar ta taka rawa sosai a faɗan da ta yi da al-Shabab a lokacin da take iko da mafi yawan yankunan tsakiyar Somaliya.

Me ya faru a faɗan?

Dakarun gwamnatin Somaliya sun kwace iko da Bohol, mai nisan kilomita 20 daga Dhuusamareeb babban birnin jihar Galmudug, inda kwanan nan ƙungiyar Ahlu Sunnah Waljama'a ta kafa sansaninta.

Fadan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da raunata wasu. Babu wanda zai iya tabbatar da ainihin adadin mace -macen da jikkatar.

Kwamishinan gundumar Dhuusamareeb Abdulrahman Ali Mohamed (Geeda-Qorow) wanda BBC ta tuntuba, ya tabbatar da fadan amma ya ƙi yin cikakken bayani game da rikicin da aka yi a Bohol, kan yawan wadanda suka rasa rayukansu da kuma waɗanda a halin yanzu ke iko da yankin.

Abdulsalan Yusuf Guled, tsohon mataimakin darakta na hukumar tsaron kasar Somaliya kuma ƙwararre kan harkokin tsaro a yankin, ya ce fadan da aka yi a Bohol gazawar gwamnatin GalMudug ce.

Jagoran jam'iyyar siyasa ta Wadajir, Abdulrahman Abdulashakuur, ya yi kira da a kawo karshen fadan da ake yi a Bohol, daga bangaren gwamnatin GalMudug.

Abdulrahman Abdulshakur ya yi kira ga gwamnatin GalMudug masu faɗa a ji da mata da matasa da dattawan gargajiya cewa tashin hankali ba zai magance matsalar ba.

"Ahlu Sunna ta ga wata dama da take jin za ta iya jan hankalin mazauna yankin. Ta ga sakamakon karuwar fadan kabilanci a yankin, wanda ya zama kalubale ga al-Shabaab, wanda gwamnatin Galmudug ta samar, don ƙwace iko da gurbin da gwamnatin da aka hamɓarar ta bari," in ji Abdulsalan Yusuf Guled.

Tun farko mene ne ya raunana Ahlu Sunna?

Ƙungiyar Ahlu Sunnah ta karbe iko da Dhuusamareeb, babban birnin yankin tsakiyar Somalia, a ranar 29 ga Fabrairu, 2020, bayan wata doguwar fafatawa.

Kungiyar ta Ahlu Sunna ta kasance tana riƙe da ikon manyan yankuna na tsakiyar yankin, tun daga shekarar 2010, inda take yaƙi da al-Shabaab, tare da taimakon sojojin Habasha. Wannan ba shi ne karo na farko da suka dawo ba.

Daga baya Ahlu Sunna ta kawar da al-Shabaab daga galibin yankin tsakiyar ƙasar.

Tun daga wancan lokacin, Ahlu Sunna ta kasance fitacciyar ƙungiyar sasantawa a yankin.

Sun fafata sosai da gwamnatin Hassan Sheikh don kafa gwamnatin Galmudug da ta daɗe tana aiki.

Sai dai, a Dhuusamareeb, Ahlu Sunna ta ayyana wata hukuma da ake kira "Jihar Yankin Tsakiya", kuma a 'yan shekarun nan an samu sabani tsakanin gwamnatin Cadaado ta wancan lokacin da Ahlu Sunna.

Amma wannan ikon daga baya ya raunana.

Sauye-sauye a Habasha

Ta fuskar siyasa da ta soji, Ahlu Sunna ta daɗe tana dogaro da dakarun Habasha makwabta, wadanda suka taimaka wajen yaki da al-Shabaab.

Gwamnatin Habasha da ta gabata, karkashin jagorancin Dr Abiy Ahmed, ta zargi 'yan Somaliya da dama da tsoma baki cikin harkokin siyasar Somaliya.

Amma sauyin da aka samu a Habasha a shekarar 2018, karkashin jagorancin Firayim Minista Abi Ahmed, ya yi tasiri sosai kan tallafin da Ahlu Sunna ke samu daga Habasha.