Matasa sun fi tsofaffi ibada a Burtaniya - Bincike

An wallafa

Wani sabon bincike ya nuna cewa matasa a Burtaniya sun fi yin ayyukan ibada da ninki biyu a kan tsofaffi.

Rahoton binciken wanda Gidauniyar Savanta Comris da ke Burtaniyar ta yi, ya nuna cewa kashi 51 cikin 100 na wadanda suka shiga gwajin 'yan shekaru 18 zuwa 34 na aikin ibada da kashi biyu cikin 100 a kan wadanda suka shiga gwajin yan sama da shekaru 55 tsawon shekara.

Binciken ya kuma nuna cewa kashi 49 na matasan da suka shiga gwajin na halartar aikin ibada a kalla kowane wata idan aka kwatanta su da kashi shida na 'yan sama da shekaru 55.

A cewar Chris Hopkins, darakta a Gidauniyar Savanta Comres, sakamakon binciken yana nuna cewa yaduwar addinai na karuwa kuma ana zamanantar da ibada ta amfani da intanet.

Sai dai ya ce "babu wasu isassun bayanai kan me ya sa matasa suka fi tsofaffi ba da karfi wurin ibada.

"Irin yadda ake samun sauyin adadin mutane a Burtaniya, akwai yiyuwar matasa na da gagarumar rawar da suke takawa wurin aiwatar da ibadarsu.

"Saboda haka watakila yadda ake samun karuwar al'umma ba abin mamaki ba ne a samu karuwar masu gudanar da addini,'' in ji Chris Hopkins.

Mr Hopkins ya bayyana cewa yaduwar addinai a Burtaniya ya sa ana samun karuwar matasa a wuraren bauta inda ya ce "abu ne mai muhimmanci a fahimci cewa akwai alaka tsakanin yaduwar addinai da kuma gudanarwa da zuwa wuraren ibada.

Masanin ya kuma kara da cewa samun yaduwar addinan da ake yi "zai sa a samu karuwar matasa da za su rika halartar addu'o'i a wuraren ibada kamar yadda wannan bincike ya nuna".

"Maria Zaman mai shekaru da 23 daga Cardiff, kuma ta fada wa BBC cewa tana sallah a kullum, kuma ta gano cewa kula da addini ya sa ta samu natsuwa a lokacin annobar cutar korona.

"A matsayina na Musulma addinina ya sa na samu natsuwa da jajircewa wurin ibada. A halin da a ke ciki shi ne kadai abun da ke da tabbas.''

Ta ci gaba da cewa "A duk lokacin da nake kallon labarai a talabijin abubuwa masu kashe jiki nake gani, kuma sai na yi addu'a nake samun natsuwa."

Maria ta ce "Na san cewa addu'o'i na da tabbas kuma ba sa canzawa. Kuma na san cewa su suke share mini hawaye kuma ginshikin rayuwata.

Ita ma Yasmine Abdel Razek mai shekaru 23 ta yadda da abin da Maria ta fada, inda ta ce ''addu'a ce dalilin da ya sa nake rayuwa.''

Ta kara da cewa "ita ce abin da a ko da yaushe take tuna mini dalilin da ya sa nake duniya."

"Addu'a ce ginshikin nasara a duniya, kuma ita ce abin da ke sa mana fatan samun tsira gobe kiyama," in ji Yasmine.

Richard Gamble wanda ya jagoranci binciken ya ce an yi shi ne da zummar musanta batun cewa Burtaniya kasa ce da al'umma ba su damu da addini ba.

"Yanzu ta bayyana karara cewa ra'ayin shiga addini na karuwa a Burtaniya," in ji Gamble.

Ya kara da cewa "Kamata ya yi a rika bai wa matasa kwarin gwiwa a kuma ja su a jiki idan suka zaburo suka rungumi addini ba wai a rika yi wa batun kallon wani bakon abu ba."

A wani bincike na daban da Jami'ar Manchester Metropolitan ta yi a wannan makon, ta gano cewa kungiyoyin addini na samun mabiya kuma hakan na da alaka da rungumar zamani ta amfani da intanet wurin gudanar da wasu nau'ukan ibada.

Hakan kuma ya bude kofa ga masu neman hanyoyi daban-daban da za su gudanar da ibadunsu cikin nutsuwa da aminci.