Iyayen yara sun koka da rashin rubuta jarabawar kammala firamare a Kano

Asalin hoton, Dalibai
Iyaye a jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya, na ci gaba da kokawa dangane da rashin sanin ranar da 'ya'yansu dake makarantun firamare dake jihar zasu rubuta jarabawar shiga makarantar sakandare wato common entrance a turance.
Iyayen na wannan koke ne yayin da aka shiga mako na uku da komawa sabon zangon karatu na bana a Kano, ba tare da sanin makomar 'ya'yansu da yanzu ake musu kallon 'yan Aji bakwai ba.
Ko da BBC ta kai ziyara wata makarantar firamare da ke Kanon don jin ta bakin daliban da suke aji shida, daliban sun shaida cewa sun kasance a aji bakwai ne saboda rashin rubuta jarrabawar kamala firamare.
Daliban sun ce duk lokacin da suka tambayi shugaban makarantarsu wato hedimasta, sai ya ce musu zaku ji kira a rediyo.

Asalin hoton, KSMOE
Daliban sun ce suna bukatar gwamnati ta dubi irin halin da suke ciki ta shirya musu jarrabawar ko sa samu su shiga makarantar sakandire.
Da BBC ta tambayi daya daga cikin malaman firamaren da ta ziyarta a Kanon, yace daliban kan zo su zauna a aji, sai su rinka yi musu bitar karatun da aka yi musu a baya.
Ya ce,"A kodayaushe mu kan tunatar da hukumar gudanarwar makarantarmu game da halin da daliban ke ciki, domin sun wuce zama a aji shida, kuma dole su matsa, sannan za a samu a dauki 'yan aji daya".
Su ma iyayen yaran dake cikin wannan yanayi sun koka inda suka ce a gaskiya zaman irin wannan yara a gida akwai matsala, suka ce ba su ga manufar gwamnati ba an ce ilimi kyauta, to amma ga yara suna zaune ba su tafi makarantar gaba da firamare ba.

Ko da BBC ta tuntubi kwamishinan ilimi na jihar ta Kano Sunusi Sa'idu Kiru, ya ce abin da ya kawo jan kafa wajen rubuta jarrabawar kammala makaranatar firamaren shi ne shirin na gwamnati wanda dole sai an tantace duk sunayen daliban da aka kawo wadanda zasu kammala firamare don tabbatar da yawan yaran.
Yace "Yara sama da dubu dari biyu da ashirin da biyu ne za su rubuta jarrabawar a fadin jihar, to amma a yanzu an kammala komai kuma gwamnati ta ware kudi, don haka a ranar 25 ga watan Satumbar,2021, za a rubuta jarrabawar".
Najeriya dai na daya daga cikin kasashen da yara ba sa zuwa makaranta musamman a jihohin dake arewacin kasar.










