'Yan Najeriya sun yi wa gwamnati ca bayan rahoton BBC na wutar Mambila

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, 'Yan kasar da dama na cewa sun yanke kauna kan gwamnatin Shugaba Buhari
An wallafa

'Yan Najeriya da dama na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan wani bincike da BBC Hausa ta gudanar da ya gano cewa gwamnatocin Najeriya na baya da na yanzu ba su yi komai a kan aikin wutar Mambila da suka yi ta ikirari ba.

Bincike da BBC Hausa ta gudanar ya bankado cewa ba a yi komai ba a wurin da aka ware domin aikin tashar samar da wutar lantarki ta Mambila da ke jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya shekara 40 da fara maganar aikin.

Tun a shekarar 1982 ne lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari aka fara maganar tashar wutar wacce a lokacin aka tsara za ta samar da wuta megawat 2,600.

Gwamnatoci da suka shude sun sake fasalta aikin wutar inda a shekarar 2012 karkashin Shugaba Goodluck Jonathan aka kara yawan megawat da tashar za ta samar zuwa 3050.

Shugaba Muhammadu Buhari ma a lokacin yakin neman zabensa ya yi ta nanata cewa zai kammala aikin wutar ta Mambila idan ya zama shugaban kasa, kuma a shekarar 2017 wasu magoya bayan gwamnatinsa sun yi ta yada wasu hotuna da ke cewa na aikin wutar ne.

Bayan sakin rahoton na BBC dai 'yan Najeriya wadanda a baya suka saka rai da cewa wannan gwamnatin za ta share musu hawaye wajen tabbatar da kammaluwar aikin wutar Mambila, sun yi ca da bayyana ra'ayoyinsu kan abin da binciken ya bankado.

Wasu ma hakuri suka dinga bayarwa da neman afuwa kan yada wasu hotuna da suka yi a baya, da ke ikirarin cewa ci gaban da ake yi na aikin wutar ne.

Me ake cewa a shafukan sada zumunta na BBC Hausa?

Bayanan bidiyo, Bidiyon binciken BBC da ya gano ba a fara aikin wutar Mambila ba tsawon shekara 40

Bayan wallafa bidiyon a shafin BBC Hausa a Facebook ranar Litinin, an kalle shi sau fiye da 300,000, an so shi sau fiye da 11,000, an yi tsokaci sau kusan 6,000 sannan an yada shi sau fiye da 12,000 cikin sa'a 24.

A Instagram kuma an kalle shi sau fiye da 65,000, an yi tsokaci sau kusan 500 duk cikin sa'a 24.

Za a iya cewa kashi 90 cikin 100 na masu tsokaci a wadannan shafukan sun yi tur ne da Allah-wadai da yaudarar da suka ce an shafe lokaci ana yi musu kan wannan aikin na Mambila.

Wasu kuma cewa suke sun ma yanke kauna da ita kanta gwamnati mai ci don ta nuna musu cewa tana ci gaba da aikin bayan ba haka ba ne.

Sannan mafi yawa sun yi ta yabon BBC Hausa kan wannan gagarumin aiki da suka ce ta yi.

Ga dai abin da wasu masu bin shafukan suke cewa:

ra'ayoyin mutane
Bayanan hoto, Ra'ayoyin mutane a shafin BBC Hausa Facebook

Abdulbasit Danmalam

Allah saka kamu ku da alkairi BBC kun kyauta wallahi ku ci gaba da tonawa azzaluman asiri. Saura ku je tashar jirgin ruwa da suka ce suna yi a Neja da Kogi.

ra'ayoyin mutane
Bayanan hoto, Ra'ayoyin mutane a shafin BBC Hausa Facebook

A Instagram kuma @badriyyasarina ta ce: Allah ka yaye mana wannan masifa ta kasar nan kamar an ce je ku kwa gani, haba shekara 40 😔😔😔! Wanda aka haifa lokacin ya isa zama shugaban kasa.

Abin da mutane ke cewa a sauran shafuka a intanet

Rabi'u Biyora ya ce:

"BBC Hausa sun cire tsoro sun yi nasu aikin da ya kamata akan aikin hasken lantarkin Mambila....

"Tambayoyin da ke zukatan al'umma suna da yawa, kuma da dukkan alamu babu wani jami'in gwamnatin da zai amsa tambayoyin....

"To ai hi kenan, yanzu dai lamarin ya fito a fili..... ."

Biyora

Asalin hoton, Rabiu Biyora Facebook

Zainab Naseer Ahmad ta ce:

Rahoton BBC Hausa a kan aikin Wutar Lantarki na Mambila abin kunya ne tsawon shekara 40, wa yake yaudarar wani?

Muna ta murnar an kusa gama aiki ashe ko farawa ba a yi ba. Yanzu duk kudin da ake warewa suna ina? Fashola da Saleh Mamman gare ku.

Wannan lamarin yana bukatar kwakkwaran binciken kuma dole gwamnatin tarayya ta fito ta yi bayani.

Muhsin Ibrahim 'ya fitar ya yanke kauna'

"Wannan zambar da ke tattare da aikin wutar Mambila gazawa ce daga dukkan gwamnatocin Najeriya da suka gabata. Don Allah kar ku ware wani shugaba ko jam'iyyarsa daga cikin wannan matsalar.

"Eh, Obasanjo ya gina wasu 'yan gidaje, kamar yadda muka gani a rahoton BBC Hausa. Sai dai yin hakan cikin shekara takwas na mulkinsa ba wani ci gaba ne na a zo a gani ba.

"A yayin da nake jinjinawa BBC Hausa kan wannan rahoton, dole ne kuma na tabbatar da cewa lamarin ya matukar bata min rai.

"Allah ya isa!"

Zainab and Muhsin

Asalin hoton, Zainab Naseer Facebook

Jaafar Jaafar

"Bankado halin da ake ciki na aikin wutar Mambila da BBC Hausa ta yi ya bayyana dalilin da ya sa muke bukatar shugaban kasa da ya fi damuwa kan ziyartar wuraren ayyukan gwamnati irin su Ogbomosho da Sabon Birni ko Arochukwu don ganin ci gaban d aidonsa ba shugaban kasa mai yawan son taron da zai dauki hotuna ko halartar taruka a New York da London da Paris ba.

Wannan layi ne