Halin da ake ciki a Zamfara makonni bayan toshe layukan waya

..
An wallafa

A Najeriya, yayin da al'umomi a jihar Zamfara ke yaba wa mahukuntan jihar bisa matakan da suka ɗauka na katse layukan sadarwa da kuma rufe kasuwannin mako-mako, a gefe guda kuma wasu na kokawa da matsin rayuwa kasancewar wasu sai sun fita kullum kafin su sami abin da za su ci da iyalansu.

Wannan na zuwa ne 'yan kwanaki da gwamnan jihar ya sanar da tsawaita matakin doɗe sadarwa a jihar har sai abin da hali ya yi.

Rufe layukan sadarwar da kuma hana kasuwannin mako-mako a jihar ta Zamfara sun sa harkoki da dama na yau da kullum sun tsaya cik, sannan harkokin kasuwanci sun ragu.

Sai dai duk da ƙorafin da wasu ke yi cewa babu walwala sosai, akasari ana maraba da matakan.

BBC ta tattauna da wata mata da ta fito daga birnin Gusau zuwa Kaduna, inda ta ce akwai jama'a da ke yabawa da wannan mataki na toshe layukan sai dai ta ce wasu suna ganin kamar an takura musu musamman ga ƴan kasuwa da sai sun fita su nemi abin da za su ci.

"Ya kamata ko da wani tallafi ne gwamnati ta bayar, kamar irin lokacin da ana harkar korona aka daina fita, ta dubi mutanen da ta san cewa za su iya samun matsala a kan rashin abinci ta taimaka musu," in ji ta.

Sai dai bayanai daga yankin Birnin Magaji na cewa tun lokacin da aka toshe layukan sadarwar, har yanzu ba a dai na kai musu farmaki ba kamar yadda wani mutumin yankin ya shaida wa BBC.

Mutumin ya yi kira ga gwamnati da ta waiwayi yankin birnin tsaba da birnin magaji kasancewar har yanzu ana kai musu hari.

Ya bayyana cewa ta kai ga yanzu ƴan bindigan suna saka musu dokoki kuma kwanaki kaɗan da suka gabata sun sace mutum uku a garin Birnin Tsaba inda ya ce duk da babu sabis ɗin waya sai da aka san yadda aka tattauna aka amso su.

Kan wannan batu dai, majalisar matasan jihar Zamfara ta ce halin da mutane ke ciki akwai bukatar gwamnatin tarayya da hukumomin jihar su samar da tallafi ga jama'a.

Munnir Haidar, wanda shi ne shi ne jagoran majalisar a jihar, ya bayyana wa BBC cewa ya kamata a fito da wani tsari wanda za a tallafa wa al'ummar jihar Zamfara.

"Bai kamata a saka mana ido ba a ce ana yaƙi da ƴan ta'adda kuma ga yaƙin yunwa da damuwa da al'umma suke ciki, waɗannan abubuwan ya kamata a yi la'akari da su tunda duk abubuwan da ake yi na yau da kullum sun tsaya cak.

"Yanzu baƙi ba su iya shigowa, babu wasu abubuwan kasuwanci saboda halin da ake ciki na matsalar tsaro," in ji shi.

Babu wani bayani daga ɓangaren hukumomin jihar ta Zamfara game da irin waɗannan korafi-korafen, kasancewar yunkurin da BBC ta yi wajen tuntuɓarsu ya ci tura.

A gefe guda kuma, a jihar Sokoto mai makwaftaka da Zamfara, 'yan bindiga ne suka auka wa ƙauyen Saminaka, cikin ƙaramar hukumar Tangaza. Wani ɗan bijilante ya shaida wa BBC cewa mutane da dama sun mutu sanadiyar harin.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ASP Sanusi Abubakar, game da wannan hari, sai dai haka ta ba cimma ruwa ba.