Rikicin APC: Inuwa Yahaya ya ce babu saɓani tsakanin shi da Danjuma Goje

An wallafa

Gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana matsayinsa kan rikicin jagorancin jam'iyyar APC a jiharsa da ke arewacin Najeriya tsakanin shi da tsohon gwamnan jihar Sanata Danjuma Goje.

Gwamna Inuwa ya shaida wa BBC cewa babu wani saɓani tsakaninsa da tsohon gwamnan Gombe Sanata Danjuma Goje, amma cewarsa dole a bi tsarin jam'iyya wurin jagoranci.

Gwamnan ya bayyana matsayinsa ne bayan wasu rahotannin da ke cewa rikici ya dabaibaye jam`iyyar APC mai mulki sakamakon wani sabani tsakanin gwamnan jihar, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya da tsohon gwamna, Senata Danjuma Goje a kan wanda ya cancanci zama jagoran jam`iyyar a jihar.

Wasu dai na cewa lamarin ya kai babu ga-maciji tsakanin jiga-jigan jam`iyyar biyu.

Amma a hirarsa da BBC, gwamna Inuwa Yahaya ya musanta, yana cewa jam`iyyarsu ta riga ta fayyace matsayin kowa a tsarinta.

"Babu wani baran-baran tsakani na da shi, illa iyaka dole ne jam'iyya ta ba kowa dama a kuma zauna cikin gaskiya," in ji gwamna Inuwa.

Batun mamayar jam'iyya ne ake ganin, ɓangarorin biyu ƴan gida ɗaya ke nuna wa juna yatsa, inda ɓangaren gwamna Inuwa ke zargin tsohon gwamnan da tafiyar da jam'iyyar a matsayin jagoranta.

Amma gwamna Inuwa ya jaddada cewa dukkaninsu ƴaƴan jam'iyya ne kuma tsarin jam'iyya ne ya kamata a bi - "idan na fita tsari sai a dawo da ni kan hanya, idan kuma akwai wanda ya fita sai ya dawo kan daidai."

Haka kuma da yake bayyana ra`ayinsa a kan rigingimun cikin gida na jam`iyyar APC a jihohi da matakin tarayya, gwamnan ya ce APC ta fi alkibla a Gombe fiye da wasu wuraren.

"Matsalar siyasa shi ne da wuya a ace ana zaune cikin zaman lafiya wani bai soki wani ba, saboda dalili na dan Adam amma muna da fahimta kuma muna kokarin ganin mun tafi cikin nasara a hangen da muke na 2023 da ma gaba," in ji gwamnan na Gombe.

Ya kuma ce batun karɓa-karɓa da ake ce-ce-ku-ce kan mulki ya koma kudancin Najeriya, "fahimta ce ta jam'iyya."

"Ba zai zama matsala nan gaba - a tsari na dimokuradiya kowa yana da dama ya fito ya yi takara ko ya nemi abu bisa bukatunsa ko don ya isa ya yi," in ji shi.