Kannywood: ‘Yan fim na jimamin mutuwar Ahmad Tage

Ahmed Tage

Asalin hoton, @Ahmad Tage Facebook

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ƴan wasan fina-finan Kannywood na alhinin rasuwar abokin sana'arsu Ahmad Tage wanda Allah Ya yi wa rasuwa.

Ahmad Tage ya rasu ne bayan jinyar rashin lafiya a asibitin Nasarawa da ke jihar Kano.

Ya fi fitowa a fina-finan barkwanci a tsawon lokacin da ya kwashe a harkar, wadda ya fara a matsayin mai daukar bidiyo, kafin daga bisani ya rikide ya zama tauraro.

'Yan uwansa sun shaida wa BBC Hausa cewa ya rasu ya bar mata biyu da 'ya'ya 21.

Tuni 'yan wasan Hausa na Kannywood suka shiga alhini tare da mika ta'aziyyarsu a shafukan sada zumunta.

Fitaccen jarumi Ali Nuhu ya sanar da labarin mutuwar Ahmad Tage a shafinsa na Instagram tare da yi masa rokon gafarar Allah.

Sakon

Taurari da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood da dama ne suka bayyana alhinin rasuwar Ahmad Tage.

Taurari irin su Saratu Daso da Maryam Booth da Abdullahi Nuhu da mawaƙa irin su Ado Gwanja sun yi wa mamacin addu'ar Allah ya jikansa.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram, Jaruma Saratu Daso ta ce mamacin wanda darakta ne kuma Jarumin kuma mai ɗaukar hoto ya rasu ne a ranar Litinin.

Daso ta yi masa addu'ar rahamar Allah.

Sakon Daso

Shahararren mawakin zamani kuma jarumin fina-finan Kannywood Ado Gwanja shi ma ya aika da ta'aziyyarsa a shafin na Instagram.

Ya ce: "Allah ya jaddada rahama a gareka mutumin kirki Allah ya sa ka huta."

Kauce wa Instagram, 1
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 1

Jarumi Saddiq Sani Saddiq ya aika da saƙon ta'aziyar rasuwar Ahmed Tage a shafinsa na Instagram inda ya ce: Allah ya maka rahama Tage, mu kuma Allah ya kyautata karshenmu."

Jaruma Maryam Booth ta sanar da rasuwar Ahmed Tega a shafinta na Instagram tare da yi masa addu'a.

Sakon Maryam Booth

Jarumi Nuhu Abdullahi shi ma ya yi wa mamacin addu'a.

Kauce wa Instagram, 2
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 2