Hannafi Dan Ibro: Abin da ya sa na gaji mahaifina
An wallafa
Latsa hoto da ke sama domin kallon hira da Hannafi Rabilu Musa:
Hannafi Rabilu Musa, dan marigayi Rabilu Musa Dan Ibro, ya ce ya gaji mahaifinsa a harkar wasan kwaikwayo ne saboda abubuwan alherin da ya yi lokacin rayuwarsa.
Hannafi, wanda shi ne na biyar cikin 'ya'yan Dan Ibro 19, ya shaida wa BBC Hausa cewa "abin da ya sa na zabi fannin wasan kwaikwayo shi ne saboda ina ganin abubuwa kala-kala da ake yi wa mahaifina kamar addu'a; rana ba za ta fito ta fadi ba tare da an yi masa addu'a ba da fatan alheri."
Ya kara da cewa ya zabi fannin barkwanci ne saboda ya zama silar yaye wa mutane oirin damuwar da ke damunsu sanna ya sanya su nishadi.