Nukiliya: Shugaban hukumar IAEA zai gana kan shirin Iran

Shugaban hukumar nukiliya ta duniya

Asalin hoton, EPA

An wallafa

Shugaban hukumar nukiliya ta duniya zai tattauna da hukumomin Iran, Lahadin nan domin kokarin kwantar da hankali a kan shirin kasar na nukiliya, wanda ke tayar da hankalin kasashen Yammacin duniya.

Wannan ita ce ziyara ta farko da shugaban hukumar nukiliyar ta duniya IAEA, Rafael Grossi ke yi a Iran din, tun bayan da sabon shugaban kasar mai tsattsauran ra'ayi Ebrahim Raisi ya hau mulki a watan da ya gabata.

A yayin ziyarar ta kwana daya shugaban hukumar ta nukiliya zai gana da mataimakin shugaban kasar ta Iran, inda tattaunawarsu za ta mayar da hankali a kan tattaunawarsu da shugaban hukumar nukiliya ta Iran din.

Shugaban zai yi kokarin kwantar da hankali ne a kan ayyukan nukiliya na Iran, wanda kasashen Yammacin duniya ke nuna damuwa a kansa.

Mista Grossi zai bukaci bayani a kan muhimman batutuwa biyu; abu na farko shi ne burbushin sinadarin yureniyom (uranium) a cibiyar nukiliyar kasar, abin da Iran din ba ta bayar da bayani a kai ba.

Sai kuma abu na biyu wanda shi ne sake barin shigar da kayar hukumar ta nukiliya ta duniya na sa ido.

Ebrahim Raisi

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A watan Yuni aka zabi Ebrahim Raisi wanda shugabannin kasashen Yammacin duniya ke gani mai tsattsauran ra'ayi ne

Gwamnatin Iran ta fara saba yarjejeniyar da aka cimma da ita ta duniya a game da bunkasa sinadarin yureniyom (uranium), bayan da tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar, sannan kuma ya kakaba wa kasar takunkumi

Tun a watan Yuni ne aka dakata da tattaunawa a kan yuwuwar sake farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran din ta 2015.

Duk wani kokari na farfado da yarjejeniyar zuwa yanzu ya ci tura kuma Iran ta ki yarda da kiran kasashen Yammacin duniya na komawa tattaunawar

Yanzu dai hukumar ta IAEA ta damu ne a kan samun damar sa ido kan harkokin nukiliya na Iran din.

Ziyarar shugaban nukiliyar na duniya a Iran ranar Lahadi za ta kasance ne gabanin taron shugabannin gudanarwar hukumar ta IAEA a Litinin.

Mista Grossi zai yi wani taron manema labarai a filin jirgin sama na Vienna da zarar ya koma daga ziyarar ta Iran.

Yayin da Iran din ta kafe kan cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne ba na soji ba su kuwa kasashen Yammacin duniya na zarginta da sɓbanin hakan, suna ganin tana kokarin kera makaman kare dangi ne.