Alhaji Saidu Umaru Namaska: Sarkin Sudan na Kontagora ya rasu

An wallafa

Allah Ya yi wa Sarkin Sudan na Kwantagora a jihar Neja, Alhaji Saidu Umaru Namaska rasuwa a ranar Alhamis.

Marigayin ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya, a cewar wasu majiyoyi daga jihar Nejan.

Sarkin Sudan na Kwantagora wanda fitaccen sarki ne a cikin masarautun arewacin Najeriya, ya rasu ne yana da shekara 84.

Sarki Saidu Umaru Namaska ya shafe shekara 47 a kan karagar Sarautar Kwantagora.

A watan Mayun da ya gabata ne 'yan bindiga suka harbe dan sarkin a lokacin da suka kai hari gonar basaraken.

Maharan sun kashe Alhaji Bashar Saidu Namaska ne a gonar da take kusa da titin Zuru a karamar hukumar Kwantagora.

A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya fitar, ya ce jihar Neja da Najeriya baki daya sun yi rashin daya daga cikin sarakunan da suka dade a kan mulki, wadanda ba za a manta da gudunmowar da suka bayar wajen zaman lafiya da hadin kai a tsakanin 'yan Najeriya ba nan da shekaru da yawa masu zuwa.

Ya ce gwamnati da al'ummar jihar Neja na mika sakon ta'aziyyarsu ga shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta jihar Alhaji Yahaya Abubakar Etsu Nupe, da kuma iyalan Alhaji Saidu Namaska da kafatanin al'uumar Kontagora.

Takaitaccen tarihin Sarkin Sudan na Kontagora

An haifi Alhaji Saidu Namaska a Kontagora ranar 31 ga watan Disamban 1937. Ya yi karatunsa tun daga firamare zuwa sakandare a Kontagora da kuma makarantar midil ta Buda har zuwa shekarar 1953.

Ya fara aiki a matsayin jami'in hukumar gandun daji a shekarar 1954. Bayan nan ya yi aiki a kotu tun daga shekarar 1968 a garuruwan Salka da Mahuta da Zuru.

Ya yi wani kwas na shari'a a Cibiyar Mulki ta Zaria a 1962 inda daga nan ya samu shaidar karatun shari'a.

A shekarar 1974 ne Alhaji Namaska ya zama Sarkin Sudan na Kwantagora na shida. Kuma kafin rasuwarsa shi ne mataimakin shugaban hukumar sarakunan gargajiya ta jihar Neja.

Marigayin ya rasu ya bar mata da 'ya'ya da jikoki har da tattaba kunni.