Gwamnan Jihar Cross Rivers Ben Ayade ya fice daga PDP ya koma jam'iyya mai mulkin kasar ta APC, tare da kira ga sauran takwarorinsa na PDP su bi sahunsa.
Gwamnan ya bayyana sauya shekar ta sa ne a gidan gwamnatin kasar da ke Calabar yayin wata tattaunawa da ya yi da shugabannin APC a JIhar.
Ayade ya ce dalilin komawar ta sa, ya zama shi ne shugaban APC a jihar, kuma duk wani abin da jam'iyyar za ta yi zai zaman karkashin ikonsa.
Yace akwai bukatar da ke kansa da sauran gwamnoni ta su hada hannu domin aiki tare da shugaba Muhammadu Buhari.
Ayade ya ce "Akwai bukatar hada karfi wuri guda domin aiki da shugaba Buhari don ganin yadda za a gyara goben kasar nan.
"Ina bukatar sauran gwamnoni da su bi sahu na su kuma fahimci mataki na na komawa APC. Muna da bukatar aiki da Buhari domin samar da hadin kai da kuma dunkulalliyar Najeriya a gobe. Akwai bukatar zama kasancewa wuri daya da Shugaban ksa domin ciyar da Najeriya gaba," in ji Ayade.
Cikin gwamnonin da suka karbe shi akwai Kayode Fayemi (Ekiti), Simon Lalong (Plateau), Hope Uzodinma (Imo) and Abubakar Badaru (Jigawa).
Duka a karkashin shugabancin Mai Mala Buni na Yobe, wanda shi ne shugaban kwamitin rikon jam'iyyar a yanzu.