Rikicin yankin Tigray: 'Miliyoyin mutane na cikin barazana saboda matakin Habasha na hana kai agaji'

An wallafa

Miliyoyin 'yan Habasha da ke zaune a arewacin kasar na cikin barazana da tagayyara, saboda hana shigar da kayan agaji yankin, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

A wani mataki da ke zaman gargadi, Majalisar ta ce hakan na tattare da matsaloli da dama.

Wani magana da yawun gwamnati ya musanta zargin cewa an hana shigar da kayan agaji yankin.

Yaƙin da aka shafe shekaru goma ana yi tsakanin dakarun gwamnati da mayakan aware na Tigray, ya jefa mutane da dama cikin halin ha'ula'i, da kuma neman dauki.

"Rayuwar mutane da dama ta ta'allaka ne kan samun damar shiga mu kai musu abinci da kayan gina jiki" in ji mukaddashin jami'in sanya ido na Majalisar Dinkin Duniya a Habasha.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane miliyan biyar da dubu dari biyu ne ke bukatar taimako, bayan samun kansu cikin wannan yanayi mafi muni cikin gwamman shekaru da suka gabata.

Hanya daya tilo da ta rage a yanzu ita ce wadda ake ratsewa ta lardin Afar, sai dai ta nan din ma cunkoso da mutanen da ke tare hanya sun yi yawa kwarai, abin da ke janyo bata lokaci.

Masu aikin agaji sun ce akwai bukatar shigar da akalla manyan motocin kayan agaji 100 zuwa Tigray, amma rabon da ko daya daga cikinsu ta samu shiga yankin tun ranar 22 ga watan Agusta.

A yankuna da dama dan taimakon da hukumomin agaji ke bayarwa ya kare ƙarkafa.

Babban jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnatin Habasha ta bude kofa ga tarin motocin da suke jira a waje.

A baya dai gwamnati ta amince cewa tana hana shigar da kayan agaji, amma saboda matsalar tsaro.

Da take magana da manema labarai a Addis Ababa babban birnin kasar, a ranar Alhamis, mai magana da yawun Firaiministan kasar Billene Seyoum ta ce manyan motoci suna kan hanyarsu ta zuwa Tigray, in ji kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ta kara da cewa hakika an rage yawan wuraren binciken ababen hawa.

Rikicin ya fara ne a watan Nuwamban da ya gabata bayan watanni da aka kwashe ana takaddama tsakanin gwamnatin Abiy Ahmed da shugabannin babbar jam'iyyar siyasa ta Tigray da ake kira (TPLF).

Ana tunanin an kashe dubban mutane kuma an tilasta wa miliyoyin mutane barin gidajensu, inda wasu suka tsere zuwa Sudan.

Yanzu fada ya bazu zuwa yankunan makwabtan Habasha na Afar da Amhara.

A farkon makon nan, shugaban hukumar agaji ta gwamnatin Amurka ya ce dakarun Tigray sun yi awon gaba da kayan da ke jibge a wani rumbun ajiyar kayan agajinsu da ke Amhara.

Kungiyar ta TPLF wacce gwamnati ta bayyana a matsayin kungiyar ta'addanci, bata maida martani kan zargin ba.