Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Tigray: Ana gano gawawwakin mutanen da aka 'jefa' a rafin Sudan
- Marubuci, Daga Vivienne Nunis
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC Africa
- An wallafa
Ana jefa gawawwakin mutanen da aka harba da bindiga da kuma waɗanda aka ɗaure hannayensu a rafin Sudan da ke kan iyaka da Habasha, kamar yadda wani likita ya shaida wa BBC.
Likitan Dr Tewodros Tefera da sauran shaidu sun yi imanin cewa gawawwakin sun fito ne daga yankin Tigray na Habasha, inda ƴan tawaye ke faɗa da sojojin gwamnati.
Ƴan sandan Sudan sun bayar da rahoton cewa sun samu jimillar gawawwaki 28.
Gwamnatin Habasha ta ce ana yaɗa labarin ƙarya kan kisan gillar da aka yi a garin Humera da ke kan iyaka.
Dr Tewodros ya shaida wa BBC cewa gomman mutane na ci gaba da ƙoƙarin tsallaka rafin Humera inda ake samun rahotannin ƙarin rikici.
Likitan na Habasha wanda ya tsere daga yankin Tigray zuwa Sudan a watan Nuwamba lokacin da rikicin ya ɓarke, ya ce a ranar litinin ya ƙirga gawa 10 da aka fito da su daga rafin Setit wanda ake kira Tekeze a Tigray.
Gawawwakin da suka ƙunshi maza da mata na cikin rafin tsawon mako ɗaya, a cewar Dr Tewodros, wanda yanzu yake da wani sansanin ƴan gudun hijira a Hamdayet, wanda ke ɗauke da ɗaruruwan ƴan gudun hijirar Habasha.
"Gawawwakin sun ruɓe kuma da wahala a iya tantance su.. amma akwai wani mutum da ke da zane a jikinsa da ke ɗauke da sunan 'Giday' da mafi yawanci aka fi kiran ƴan Tigray," in ji shi.
Likitan ya ce sabbin ƴan gudun hijira da suka shigo sansanin sun shaida wa jami'ai cewa ana ƴan sa-kai da ke samun goyon bayan gwamnati sun kama mutane da dama daga yankin Amhara na Habasha mai maƙwabtaka da Tigray.
BBC ba ta tabbatar da waɗannan zarge-zargen ba.
Faɗa ya ƙazance tun watan Yuni lokacin da ƴan tawayen Tigray suka ƙwace ikon yawancin yankin.
Tun lokacin hukumomi daga sassan ƙasar ke ƙoƙarin shiga yaƙin.
Ma'aikatan agaji da ke ƙoƙarin samun isa yankn Tigray sun fuskanci hare-hare da kuma hana su shiga yankin.
Shugaban hukumar agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya soki jami'an gwamnati da ke zargin ma'aikatan agaji da nuna goyon bayan wani ɓangare - da kuma taimaka wa ƴan tawayen Tigray da makamai.
Martin Griffiths, wanda ya bai daɗe da kammala ziyarar kwanaki shida ba a ƙasar, ya ce waɗannan zarge-zargen na da "matuƙar hatsari" waɗanda ya kamata a yi gaggawar dakatarwa.
Gwamnatin Habasha ta ayyana TPLF a matsayin ƙungiyar ƴan ta'adda, amma kuma ƴan tawayen sun ce ƙungiyar ita ce halattaciyar jam'iyyar yankin.
TPLF ta dawo daga rakiyar Firaiministan Habasha kan sauye-sauyensa na siyasa, ko da yake ta ƙwace sansanonin soji a Tigray da suka yi tasiri ga farmakin watan Nuwamba.
Wasu labarai kan rikicin Tigray