Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Haaland, Woodward, Ronaldo, Olmo

Erling Braut Haaland, ya yi farin jini ga kungiyoyi da dama

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Dan wasan Borussia Dortmund da kasar Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 21, zai ci gaba da kasancewa babban wanda Manchester United ke fatan saye a bazara ta gaba duk kuwa da komawar tsohon tauraronta Cristiano Ronaldo mai shekara 36 daga Juventus. (ESPN)

Mataimakin shugaban Manchester United mai barin gado Ed Woodward shi ya taka muhimmiyar rawa wajen dawo da kyaftin din na Portugal Old Trafford. (Manchester Evening News)

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, OTHERS

Ana sa ran dan wasan tsakiya na Sifaniya Saul Niguez, mai shekara 26, ya sa jesi mai lamba 17 a Chelsea bayan da ya koma can a matsayin aro daga Atletico Madrid a ranar karshe ta cin kasuwar 'yan wasa. (Star)

Barcelona za ta kara kokarin sayen dan wasan tsakiya Dani Olmo, mai shekara 23, a watan Janairu bayan da RB Leipzig ta ki sayar mata da shi a ranar karshe ta sayar da 'yan wasa da aka rufe a kan fam miliyan 50. (Mail)

Dani Olmo

Asalin hoton, OTHERS

Leicester da Southampton da Nottingham Forest sun yi kokarin sayen dan bayan Middlesbrough Djed Spence, mai shekara 21 sai dai a dab da kasuwar sayar da 'yan wasan na shirin rufewa ne suka taya dan Ingilar. (Northern Echo)

Nottingham Forest ta yi nasarar karbar Djed Spence aro tsawon kaka daya

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto, Nottingham Forest ta yi nasarar karbar Djed Spence aro tsawon kaka daya

Kocin Tottenham Nuno Espirito Santo ya ba wa sabon dan wasan da suka saya Emerson Royal, mai shekara 22, tabbacin cewa zai taka muhimmiyar rawa a kungiyar, kafin dan bayan dan Brazil ya yarda ya bar Barcelona. (Marca)

Emerson zai yi gogayya wajen zama babban dan baya a Tottenham tare da Japhet Tanganga da Matt Doherty

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United da Liverpool da kuma Arsenal sun shirya gogayya wajen sayen dan wasan tsakiya na Brighton kuma dan Mali Yves Bissouma mai shekara 25, a watan Janairu. (Mirror)

Yves Bissouma

Asalin hoton, Getty Images

An bar dan bayan Chelsea Malang Sarr, mai shekara 22 zaman kasha-wando, ba ta yi bayan shirin mika shi aro ga kungiyar Greuther Furth ta gasar Jamus, Bundesliga ya ci tura a ranar karshe ta kasuwar saye da sayar da 'yan wasa da aka rufe. (Mail)