A yanayi na ba saban ba, Buhari ya je ta'aziyya da kansa

Buhari

Asalin hoton, Instagram/ Buhari Sallau

Bayanan hoto, Buhari ya yaba wa Ahmed Joda bisa rawar da ya taka wajen ci gaban Najeriya
An wallafa

A wani mataki na ba saban ba, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya je ta'aziyya da kansa bai aika da sako ba.

Shugaban ya je birnin Yola na jihar Adamawa ranar Juma'a domin yin ta'aziyyar rasuwar Malam Ahmed Joda, tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Mulkin Sojin Najeriya kuma gogaggen ma'aikacin gwamnati.

Malam Joda ya rasu ne ranar Juma'ar makon jiya yana da shekara 91 a duniya.

Alhaji Ahmed Joda ya yi aiki a bangarori daban-daban a Lardin Arewa kuma daga bisani ya rike mukamai da dama a gwamnatin tarayya.

Yana daya daga cikin mutanen da ke yi wa lakabi da Super Permanent Secretaries, wato manyan sakatarorin gwamnati, a zamanin mulkin soja ta Janar Yakubu Gowon.

Ahmed Joda ya kasance shugaban tawagar wakilan Buhari da ta karbi mulki daga gwamnatin Goodluck Jonathan bayan zaben 2015.

Shugaban na Najeriya ya isa birnin Yola ne da safiyar Juma'a inda ya yi wa Masarautar Adamawa ta'aziyyar rasuwar "fitattun 'ya'yanta uku ciki har da marigayi Alhaji Ahmed Joda," kamar yadda mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Buhari Sallau ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Shugaba Buhari ya ga gana da Lamidon Adamawa Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha da gwamnan jihar Ahmadu Umar Fintiri da sauran manyan jami'an gwamnati.

Wannan ziyarar ta'aziyyar ta kasance ta ba saban ba, musamman idan aka yi la'akari da cewa ba a cika ganin Shugaba Buhari yana zuwa ta'aziyyar mutuwar fitattun 'yan kasar da kansa ba tun da ya hau karagar mulki a shekarar 2015. Wasu ma na cewa ba su iya tuna wani lokaci da suka ga shugaban a wurin ta'aziyya da kansa.

A baya dai, shugaban yana aikawa ne da manyan jami'an gwamnati kamar su Sakataren Gwamnatin Tarayya da ministoci da kuma manyan jami'an sojin domin yin ta'aziyya ga fitattun 'yan kasar da suka riga mu gidan gaskiya. Haka nan yana yawan fitar da rubutattun sakonnin ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu.

Wannan lamari kan jawo masa suka daga bangarori daban-daban, inda wasu suke ganin ya kamata ya rika zuwa da kansa wasu daga cikin wuraren ta'aziyyar da yake yin aike.

Sai dai fadar shugaban ta sha kare shi tana mai cewa ba dole ne shugaban ya je ta'aziyya da kansa ba idan ya aika da tawaga ta wadatar.

Ko a watan Mayu, 'yan kasar da dama sun soki Shugaba Buhari bisa rashin halartar jana'izar babban hafsan sojin kasar Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan jami'an soji wadanda suka mutu sakamakon hadarin jirgin saman soji a Kaduna.

Wasu daga cikin fitattun da Shugaba Buhari bai halarci jana'iza ko ta'aziyyarsu ba su hada da wasu aminansa kamar su Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Malam Ismai'ila Isa Funtua, da kuma AVM Muktar Mohammed. Wasu ma na ambaton rashin zuwa ta'aziyyar Isyaka Rabi'u, fitaccen malamin addinin Musulunci a Kano.

Kazalika bai je ta'aziyyar tsohon gwamnan jihar Lagos, Lateef Jakande, jigo a jam'iyyar APC, Tony Momoh, Sam Nda-Isaiah da sauransu ba. To amma dukkansu ya aike da sakonnin ta'aziyya ga iyalansu.