Ƙungiyar Tagwaye a Jihar Kano ta yi taronta na shekara

An wallafa
A ranar Lahadi ne kungiyar tagwaye ta Jihar Kano ta yi taronta na shekara-shekara a birnin da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Shugaban ƙungiyar, Hassan Tijjani, ya ce suna zaman ne saboda taimakon juna da kuma al'umma baki ɗaya.

Shekara 15 kenan da kafa ƙungiyar kuma kakakinta Hassan Indabawa ya ce sukan haɗa kuɗi duk wata domin taimaka wa waɗanda ke da buƙata a cikinsu.

"Akwai marasa sana'a ko neman shiga jami'a, duk muna shiga mu taimaka," a cewarsa.

"Duk wata muke haɗa kudi domin taimaka wa juna."

Ya yi kira ga gwamnati da ta shiga lamarinsu domin taimakawa.

Ya zuwa yanzu, babu wata ƙididdiga da ke tabbatar da yawan tagwaye a Kano ko Najeriya baki ɗaya.







