Kasuwar 'yan kwallon kafa; Makomar Varane, Vinicius, Kane, Henderson, Lukaku, Icardi, Trippier

Varane da Pogba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kungiyoyi da dama na son Varane
An wallafa

Ana sa ran Manchester United za ta gabatar da tayin sayen dan bayan Real Madrid Raphael Varane, mai shekara 28, a hukumance a wannan makon, amma kuma ana ganin ba za ta sayi dan wasan da yake da sauran shekara daya kawai a kwantiraginsa ba kan fam miliyan 50. (Jaridar Daily Mail)

Kungiyoyi da yawa na son dan wasan na tawagar Faransa, inda Chelsea ke duba yuwuwar bin layin United da Paris St-Germain wajen zawarcin dan bayan. (Jaridar Marca)

Haka kuma an bai wa Manchester United damar sayen dan wasan gefe na Real Madrid, dan Brazil Vinicius Junior, mai shekara 21, yayin da kungiyar ta Sifaniya ke kokarin tara kudin da za ta sayi dan wasan gaba na Faransa da Paris St-Germain Kylian Mbappe. (Mirror)

A ranar 29 Satumba 2019 Vinicius Junior ya fara taka wa Real Madrid leda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar 29 Satumba 2019 Vinicius Junior ya fara taka wa Real Madrid leda

Abokan wasan Harry Kane na tawagar Ingila na ganin dan wasan mai shekara 27, ba zai bi Tottenham wasannin gwaji na shirin tunkrarar sabuwar kaka ba, domin ya matsa tafiyarsa Manchester City a bazaran nan. (The Telegraph)

Tottenham na son sayen dan wasan tsakiya na Roma Lorenzo Pellegrini, mai shekara 25, ko da yake ba a san ko dan wasan na tawagar Italiya zai so tafiya Ingila ba. (Gazzetta dello Sport)

Fenerbahce na tattaunawa da West Ham a kan cinikin dan wasan na gefe, dan Ukrain Andriy Yarmolenko mai shekara 31 a kan fam miliyan biyu. (Football Insider)

Messi da Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Messi da Mbappe

Dan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson, mai shekara 31, na shirin kulla sabuwar yarjejeniya da Liverpool. Kwantiragin kyaftin din Reds din na yanzu zai kare ne a Anfield a 2023. (Mirror)

Dan bayan Brazil Alex Telles ya yi watsi da maganganun da ake yi cewa zai bar Manchester United a bazaran nan , inda ya ce shi dai yana jin dadin zamansa a Old Trafford.

Ana alakanta dan wasan mai shekara 28, wanda ya koma United daga Porto a shekarar da ta wuce da Roma da kuma Inter Milan. (Goal)

Wakilin Romelu Lukaku Federico Pastorello ya tabbatar wa magoya bayan Inter Milan cewa dan gaban na Belgium mai shekara 28, ba zai bar San Siro a bazaran nan ba duk da matsalolin kudi da kungiyar ke ciki. (FCInterNews)

Romelu Lukaku ya ci wa Inter Milan kwallo 27 a kakar da ta kare

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Romelu Lukaku ya ci wa Inter Milan kwallo 27 a kakar da ta kare

Mauro Icardi na da damar barin Paris St-Germain domin tafiya Juventus a bazaran nan. Dan wasan na gaba, dan Argentine mai shekara, 28, ya shafe shekara bakwai a Serie A a Inter Milan, kafin komawarsa kungiyar ta Faransa a 2019. (Footmercato).

Juventus na sha'awar sake sayen dan wasan tsakiya na Bosnia Miralem Pjanic, wanda ba a sa shi a wasa sosai tun da ya koma Barcelona daga kungiyar ta Italiya a 2020. (Mundo Deportivo)

Idan dai har Liverpool na son ta riga Borussia Dortmund sayen dan gaban PSV Eindhoven Donyell Malen, to sai ta yi sauri da gaske. Kafin Jurgen Klopp ya sayi dan wasan mai shekara 22, dole sai ya rage 'yan wasan da ba ya amfani da su sosai daga kungiyar. (Daily Express)

Shirin ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, Brexit, zai iya taimaka wa Manchester United dauko dan bayan Atletico Madrid da Ingila Kieran Tripper, mai shekara 30, saboda dokokin gasar La Liga a kan 'yan wasan Ingila sun kawo karshe a kwanan nan. (Daily Express)

Tripper ya koma Atletico Madrid ne daga Tottenham a watan Yuli na 2019

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tripper ya koma Atletico Madrid ne daga Tottenham a watan Yuli na 2019

Yayin da shirin ficewar Birtaniyar daga Turai zai iya amfanar United a nan, shi kuwa Gareth Bale, mai shekara 32, na cikin rashin tabbas bayan zaman aron da ya yi a Tottenham ya kare, saboda Real Madrid na da damar daukar 'yan wasa uku ne kawai wadanda ba daga wata kasa ta Tarayyar Turai suke ba, kamar yadda dokar La Liga ta tanada. (Mirror)

Idan Trippier ya tafi United, Atletico Madrid za ta nemi sayen dan bayan Norwich da tawagar 'yan kasa da shekara 21 ta Ingila Max Aarons, wanda kila sai zakarun na Sifaniya sun kashe fam miliyan 25 su same shi. (Mirror)

Dan wasan tsakiya na Barcelona Riqui Puig ya yi watsi da tayin kungiyoyi da dama da ke sonsa, inda dan Sifaniyar mai shekara 21 ya gwammace ya tsaya ya yi fafutukar neman gurbi a kungiyar ta Nou Camp, karkashin kociyan Ronald Koeman. (Sport)

Golan Bournemouth Asmir Begovic ya tsallake gwajin lafiyarsa a shirin komawar da dan Bosniyar mai shekara 34 ke yi na tafiya Everton. (Talksport).

Crystal Palace na shirin doke Leeds a zawarcin dan gaban Peterborough, dan Portugal Adler Nascimento, mai shekara 16, wanda a baya Wolves da Brighton suka so shi. (Daily Mail)