Boko Haram: Sojin Najeriya sun saki mutum 1000 da aka zarga da hannu a kungiyar

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Rundunar sojin Najeriya ta ce mutanen da ta saka ba tubabbun 'yan Boko Haram ba ne
An wallafa

Rundunar sojin Najeriya ta saki fiye da mutum 1000 da aka zarga da kasancewa 'yan kungiyar Boko Haram.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Alhamis ta bakin mai magana da yawunta, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ta ce an saki mutanen ne bayan "an wanke su" daga zargin zama 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Rahotanni sun nuna cewa an tsare mutanen ne a wani sansanin soji da ke birnin Maiduguri kafin a mika su ga gwamnatin jihar Borno ranar Laraba.

Sanarwar ta ce mutanen da aka zarga da zama 'yan kungiyar ta Boko Haram su 1009 sun fuskanci tambayoyi masu tsauri da "cikakken bincike" kafin a wanke su daga zargin.

Sai dai rundunar sojin ta musanta jita-jitar da ake watsawa cewa mutanen tsofaffin mayakan Boko Haram ne.

Ba a san tsawon lokacin da mutanen suka kwashe a tsare a hannu na sojoji ba.

Amma a shekarar 2017 ne gwamnatin Najeriya ta soma wani gudanar da wata shari'a kan kusan mutum 6000 da take zargi da hannu a kungiyar- an tsare da dama daga cikinsu tsawon shekaru ba tare da an tuhume su da aikata wani laifi ba.

An samu wasu daga cikin wadanda aka yi wa shari'a da laifi inda aka yanke musu hukunci yayin da wasu kuma ana sallame su bayan sun tuba ko da yake sai da aka yi musu horo na fita daga ayyukan ta'addanci.

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar kwanakin baya ya nuna cewa rikicin na Boko Haram wanda aka kwashe sama da shekaru 10 ana yi ya yi sanadin mutuwar kusan 350,000.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce tana yin bakin kokarinta wajen murkushe kungiyar.

A kwanakin baya rahotanni suka tabbatar da mutuwar shugaban wani bangare na kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau, sakamakon tashin bam din da ya yi da ke jikinsa don kin yi mubaya'a ga daya bangaren na kungiyar.