Halin taskun da ƴan Najeriya mazauna Oman ke ciki

Asalin hoton, NIDCOM
Wasu ƴan Najeriya mazauna ƙasar Oman, kimanin 90 sun ce sun shiga halin tsaka mai wuya saboda rashin sabunta musu fasfo bayan ƙarewar wa'adinsu, a wannan lokaci da ƙasar ke cikin dokar kulle saboda annobar Korona.
Wani da BBC ta zanta da shi, Abdulƙadir Abdulwahab ya ce da yawansu kuma suna fuskantar barazanar rasa ayyukansu a kamfanoni da ma'aikatun ƙasar saboda rashin ingantaccen fasfo.
A cewarsa, lamarin ya jefa su cikin matsala sosai saboda rashin fasfo ɗin ka iya sa su shiga garari - "aiki da wahalar samu ga iyali, a taimaka mana muna cikin matsala". in ji Abdulwahab.
Ya ce annobar korona ce ta taɓarɓara halin da suke ciki sannan kuma ƙasashe daban-daban suna da dokokin da suka sa don hana bazuwar cutar
"Yawancinmu muna ta tunanin cewa idan za a bari mu fita mu je sannan mu dawo cikin sauki, ai gwara mu je Najeriya ɗin amma yanzu an rufe ko ina, Najeriya tana daga cikin ƙasashen da aka hana shigowarsu, duk wanda ya je Najeriya ba zai shigo nan ba". in ji shi.
Amma ya ce wannan dokar bai shafi jami'an Najeriya da ke ofishin jakadancin kasar ba, "ba wani takunkumi da zai hana su shigowa Oman su yi mana aiki".
Sai dai hukumar kula da al'amuran ƴan Najeriya mazauna ƙetare ta ce ba ta da labarin halin da waɗannan mutane suke ciki.
Jami'ar yada labarai a hukumar, Khadija Shehu Bamalli ta shaida wa BBC cewa sun samu korafe-korafe daga wasu daga cikin yan Najeriyar da ke Oman ɗin.
Ta ce irin lamarin ya taɓa yan Najeriya da dama da ke wasu ƙasashen ba wai Oman ba kaɗai.
A cewarta, shugabar hukumarsu, Abike Dabiri Erewa ta tattauna da ofishin da ke ba da fasfo da kuma ministan harkokin cikin gida kan yadda za su shawo kan matsalar da nufin taimaka wa yan Najeriyar da suke cikin wani hali a wasu ƙasashen.











