Cutar amai da gudawa ta kashe mutum 119 a Kano

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar Lafiya ta Kano da ke arewacin Najeriya ta ce mutum sama da dubu uku ne suka kamu da cutar amai da gudawa a jihar daga ranar 5 ga watan Maris na 2021 zuwa yanzu .
Ma'aikatar lafiyar ta shaida wa BBC cewa mutum 119 ne daga cikinsu suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.
Mataimakin daraktan kula da sashen lafiyar al'umma na Ma'aikatar Lafiyar, Dr. Bashir Lawan, ya ce an samu bullar cutar amai da gudawar a kananan hukumomi 33 daga cikin 44 na jihar.
Ya kara da cewa mutum sama da dubu biyu ne suka warke daga cutar, yana mai cewa ana ci gaba da kula da sama da mutum dari a asibitoci daban-daban da ke jihar.
"Daga wajen 5 ga watan uku na wannan shekarar kawo yau, 22 ga watan 6 mun samu mutum 3,209 wadanda suka kamu da wannan ciwo, mun samu warkar da mutum 2,996, a yau din nan akwai mutum 105 da muke kula da su a mabambantan kananan hukumomi," in ji shi.
Dr. Lawan ya ce kananan hukumomin Gaya da Bichi ne kan gaba wajen masu fama da cutar.
Sai dai ya ce an sami raguwar masu kamuwa da cutar saboda matakan da hukumomi suke dauka wajen shawo kanta.
A cewarsa, matakan sun hada da fadakarwa game da tsafta ta kai da ta muhalli da makamantansu.
Mene ne yake haddasa amai da gudawa?
Tuni dai likitoci a jihar ta Kano suka bazama wajen ci gaba da wayar da kan jama'a kan abubuwan da suka kamata a yi domin kauce wa kamuwa da amai da gudawa.
Dr. Ya'u Sulaiman, wani kwararren likita a jihar ta Kano, ya shaida wa BBC yadda ake kamuwa da cutar kwalara.
"Abubuwan da suke haddasa cutar kwalara kwayoyi ne na cuta wadanda yawanci ake ci a cikin abinci wanda ba a tsaftace ba lokacin da ake hada shi, ko kuma a lokacin da ake amfani da shi," a cewarsa.
Ya ce ya kamata a tsaftace kayan marmari ko ganyayyaki da ake amfani da su.
A cewarsa, alamomin kamuwa da cutar sun hada da gudawa da amai da ciwon ciki da kuma yaushin jiki, alamun da ke nuna cewa ruwa yana karewa a jikin wanda ya kamu da cutar.
A baya bayan nan dai an sami bullar cutar amai da gudawa a wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya, ciki har da Bauchi da ke makwabtaka da Kano, inda cutar ta yi sanadiyar mutuwar mutum kusan 20.










