Hotunan yadda Tsaunin Nyiragongo ya rufta a DRC

An wallafa

Dubban mutane ne suka tsere daga muhallansu a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo bayan da wani tsauni ya yi aman wuta kusa da birnin Goma.

Aman wutar da dutsen ya yi ya hankada giza-gizan birnin da ke gabashi, wanda ke da yawan mutane miliyan biyu.

Mutane sun yi ƙoƙarin kashe wutar a lokacin da ruwan ya kwarara ya mamaye wasu ɓangarorin birnin da tituna.

Ana iya ganin wuta a tsakankanin gine-gine a birnin.

Mazauna birnin sun tsere da katifunsu da sauran kayansu.

Bayan isa unguwannin da ke wajen birnin da filin jirgin sama da ke gabashi, a yanzu ruwan wutar ya daina kwarara.

Dubban ƴan Congo, ciki har da yara da tsoffi sun nemi mafaka a maƙwabciyarta Rwanda a lokacin da dutsen ya yi amai.

A nan suna bacci da kayayyaki a bisa wani titi a garin Gisenyi a iyakar Jamhuriyar Demokuraɗiyyar Congo.

Tsaunin Nyiragongo na ɗaya daga cikin tsaunuka da ke aman wuta a duniya - inda a nan a ke iya ganinsa dada Tsibirin Tchegera a kan Tafkin Kivu a wajen Goma.

Duka hotunan na da haƙƙin mallaka.