Israel-Gaza: Jami'in Hamas ya ce 'za a daina faɗa cikin kwana ɗaya ko biyu'

Palestinian sisters sit on an unexploded missile fired by Israeli warplanes in Gaza

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Palestinian sisters sit on an unexploded missile fired by Israeli warplanes in Gaza
An wallafa

The Gaza fighting began after weeks of rising Israeli-Palestinian tension in occupied East Jerusalem that culminated in clashes at a holy site revered by both Muslims and Jews. Hamas, which controls Gaza, began firing rockets after warning Israel to withdraw from the site, triggering retaliatory air strikes.

Wani babban jami'in ƙungiyar Hamas ya ce yana sa ran Isra'ila da mayaƙan da Gaza za su cmma yarjejeniyar tsagaita wuta "cikin kwana daya ko biyu" yayin da fadan ya ke ci gaba da ƙaruwa.

Sai dai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce "a shirye ya ke ya ci gaba da kai hare-hare, har zuwa lokacin da aka "samar da zaman lumana da yanayin tsaro ga 'yan Isra'ila".

Isra'ila ta kai hare-hare fiye da 100 ta sama kan wasu sansanonin Hamas a arewacin Gaza da sanyin safiyar Alhamis.

A nasu bangaren kuwa, mayakan Falasdinu sun mayar da martana ta hanyar harba rokoki kan wasu garuruwa a cikin Isra'ila.

At least 227 people, including more than 100 women and children, have been killed in Gaza so far, according to its health ministry. Israel has said at least 150 militants are among those killed in Gaza. Hamas does not give casualty figures for fighters.

In Israel 12 people, including two children, have been killed, its medical service says. Israel says some 4,000 rockets have been fired towards its territory by militants in Gaza.

A kalla mutum 227 ciki har da mata 100 da kananan yara su ka rasa rayukansu a Gaza kawo yanzu.

A Isra'ila kuwa mutum 12 cikinsu har da kananan yara biyu jami'an kiwon lafiyar kasar su ka ce an kashe.

An Israeli soldier looks on as Israel's Iron Dome anti-missile system intercept rockets launched from the Gaza Strip

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata sojar Isra'ila na kallon yadda makaman kariya na Isra'ila mai suna Iron Dome ke kakkabo rokokin da mayakan Hamas ke harbawa zuwa cikin Isra'ila

Wata majiyar tsaro daga Masar ta fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa bangarorin biyu sun amince da tsagaita wuta.

A ranar Laraba shugaban Amurka JOe BIden ya yi magana da Mista Netanyahu a karo na hudu tun da wannan rikicin ya fada.