Laylatul Qadr: Hotunan yadda Musulman duniya ke neman dacewa da daren rahama

An wallafa

Asabar 20 ga watan Ramadan, wadda ta yi daidai da 1 ga watan Mayun 2021, ita ce rana ta farko da mafi yawan Musulman duniya suka fara tsayuwar dare da zummar samun dacewa da daren Lailatul Ƙadari.

A Musulunci, ana yi wa daren kallon wanda ya fi wata 1,000 daraja kasancewar a cikinsa aka fara saukar da AlƘur'ani mai tsarki.

Mun zabo muku hotunan yadda Musulmai a sassa daban-daban na duniya suke fafutukar dacewa da wannan dare mai tsarki:

Worshippers place the Koran, Islam's holy book, on their heads during prayer rituals of Laylat al-Qadr (Night of Destiny) which marks the night in which the holy Koran was first revealed to the Prophet Mohammed, at the Imam Ali shrine in the holy Iraqi city of Najaf, on May 1, 2021. (Photo by Ali NAJAFI / AFP) (Photo by ALI NAJAFI/AFP via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu masu ibada kenan suka ɗora Ƙur'ani a kansu yayin da suke addu'a don dacewa da daren Lailatul Ƙadari a ranar Asabar a Hubbaren Sayyadi Ali da ke garin Najaf na Iraƙi
Madina

Asalin hoton, Haramain Sharifain

Bayanan hoto, Yadda masallata suka duƙufa kenan a Masallacin Annabi na Madina domin dacewa da daren a ranar Lahadi
Iranians wearing face masks as COVID-19 prevention attend ritual prayers in the rain, for Laylat al-Qadr (Night of Destiny) one of the holiest nights during the Muslim fasting month of Ramadan, outside the Imamzadeh Ainali-Zeinali mosque in the capital Tehran, on May 1, 2021. (Photo by ATTA KENARE / AFP) (Photo by ATTA KENARE/AFP via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu mata kenan sanye da takunkumi yayin da suke halartar wurin addu'a a cikin ruwa don dacewa da daren Lailatul Ƙadri a wajen Masallacin Imamzadeh Ainali-Zeinali da ke birnin Tehran na Iran ranar Asabar
Makkah

Asalin hoton, Haramain Sharifain

Bayanan hoto, Sai a daren Lahadi aka fara sallar dare a Masallacin Harami na Makkah, inda ɗaruruwan Musulmi suka shafe daren don gudanar da ibada
MAY 02: Students wear protective masks light candles as they prepare for read the Quran during ritual Nuzulul Quran and Laylat al-Qadr (Night of Destiny) which marks the night in which the holy Quran was first revealed to the Prophet Mohammed at the Nurul Hidayah Al-Mubarokah boarding school on May 2, 2021 in Boyolali, Central Java, Indonesia. Laylat al-Qadr is was one of the odd-numbered nights of the last ten days of Ramadan. Millions of Muslims around the world fasting from dawn to dusk for a month. Ramadan, the ninth month of the Islamic calendar is a month of fasting, prayers and recitation of the Quran. (Photo by Ulet Ifansasti/Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu ɗalibai mata kenan a makarantar kwana mai suna Nurul Hidayah Al-Mubarokah da ke Indonesia suna shirin fara karanta Ƙur'ani cikin hasken kendir don dacewa da wannan dare mai albarka ranar Lahadi
MAY 02: Students read the Quran by candlelight during ritual Nuzulul Quran and Laylat al-Qadr (Night of Destiny) which marks the night in which the holy Quran was first revealed to the Prophet Mohammed at the Nurul Hidayah Al-Mubarokah boarding school on May 2, 2021 in Boyolali, Central Java, Indonesia. Laylat al-Qadr is was one of the odd-numbered nights of the last ten days of Ramadan. Ramadan, the ninth month of the Islamic calendar is a month of fasting, prayers and recitation of the Quran. (Photo by Ulet Ifansasti/Getty Images)

Asalin hoton, Ulet Ifansasti

Bayanan hoto, Ɗalibai kenan da ke fatan dacewa da Lailatul Ƙadari ta hanyar karatun Ƙur'ani a Indonesia ranar Lahadi
An Iranian woman takes part in ritual prayers in the rain for Laylat al-Qadr (Night of Destiny), one of the holiest nights during the Muslim fasting month of Ramadan, outside the Imamzadeh Ainali-Zeinali mosque in the capital Tehran, on May 1, 2021. (Photo by ATTA KENARE / AFP) (Photo by ATTA KENARE/AFP via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata kenan a Iran take addu'a a cikin ruwa a yunƙurinta na dacewa da daren ranar Asabar
Worshippers take part in prayer rituals of Laylat al-Qadr (Night of Destiny) which marks the night in which the holy Koran was first revealed to the Prophet Mohammed, at the Imam Ali shrine in the Iraqi city of Najaf, on May 1, 2021. (Photo by Ali NAJAFI / AFP) (Photo by ALI NAJAFI/AFP via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu ibada a wajen Hubbaren Sayyadi Ali ranar Asabar