Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hoton abincin iyali ya lashe gasar hotuna ta duniya
Hoton wasu ma'aurata da ɗansu suna dafa abinci fuskokinsu cikin farin ciki da annashuwa ya lashe babbar gasar hotunan abinci ta duniya da aka yi a China
An bayyana sunan Li Huaifeng a matsayin wanda ya lashe gasar 'Pink Lady Food Photographer of the Year 2021' wanda ya saka ma hotonsa suna 'Taste, taken in Licheng, Shanxi'.
"Wannan hoton ya fita daban da sauran hotuna saboda yadda aka yi amfani da haske da kuma yadda aka shirya daukarsa," a cewar Caroline Kenyon wadda ita ce ta kirkiro gasar.
"Amma kuma abin da ya ƙara fito da shi da ke da muhimmanci shi ne irin abin da yake koyarwa da kuma yadda yake sosa zuciya idan ka nutsu ka kalle shi."
"Yana nuna yadda aka shafe shekara ana rayuwa a lokacin kullen korona, a gidajen da ba su da wadata sosai."
"Da zarar ka kalli hoton za ka fahimci akwai soyayya da kuma shaƙuwa tsakanin uwa da ɗanta."
"Kuma hakan ya fito da cewa ƙayataccen hoto ba yana nufin sai wani abun mamaki ko tsoro ba."
"Babu shakka wannan hoto ne da zai tsaya maka a rai irin yadda aka tsara shi," in ji Caroline.
A bana ne wannan gasa ta cika shekaru 10, kuma alƙalan gasar sun karɓi hotuna 10,500 daga ƙasashe 70 a fadin duniya inda aka sanar da waɗanda suka lashe gasar kai tsaye ta intanet.
Ga wasu daga cikin hotunan da suka lashe gasar a matakai daban-daban.
Yadda nake samar da busasshiyar kuɓewa daga F Dilek Uyar, Turkiyya
Hoton wasu ma'aurata da ke tsoron tartsatsin wutar da ke kan tunkuzar bikin aurensu : daga John Armstrong-Millar, a Faransa
Kayan gona: daga Martin Grünewald, Jamus
Yadda ake samar da taliyar indomie: daga Abdul Momin, Bangladesh
Yadda aka sarrafa tufa tare da biredi: daga Natalia Bogubowicz, Poland
Abincin kan titi: daga Viet Van Tran, Vietnam
Gwaiba ta musamman daga Harriet Harcourt, Australiya
Abincin gargajiya: daga Sarah Blandford, Birtaniya
Sarauniyar wata daga: Deborah Trocchia, Italiya
Babu maraya sai rago: daga Joseph P Smith, Malta
Abincin bola: daga Md Mahabub Hossain Khan, Bangladesh
Dukkan hotunan na Pink Lady Food Photographer of the Year 2021 ne.