Hotunan Afirka na mako: daga ranar 16-22 ga watan Afrilun 2021

An wallafa

Mun zabo muku fitattun hotunan Afirka na wannan makon:

Babacar Kor, mamba a kungiyar Musulami ta Baye Fall da ke kasar Senegal yana tsaye a kofar shagonsa a garin Ndem ranar Laraba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Babacar Kor, mamba a kungiyar Musulami ta Baye Fall da ke kasar Senegal yana tsaye a kofar shagonsa a garin Ndem ranar Laraba.
A ranar Asabar aka kammala wasan wutar da aka kwashe mako guda ana yi na bikin al'adu na Popo a kasar Ivory Coast...

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Asabar aka kammala wasan wutar da aka kwashe mako guda ana yi na bikin al'adu na Popo a kasar Ivory Coast...
Bikin wanda aka gudanar a Bonoua ya hada da na nunin al'adun al'umar Aboure, inda suke raye-raye da gasar kyau da makamantansu...

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Bikin wanda aka gudanar a Bonoua ya hada da na nunin al'adun al'umar Aboure, inda suke raye-raye da gasar kyau da makamantansu...
Dandazon jama'a ne galibi suke halartar bikin...

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Dandazon jama'a ne galibi suke halartar bikin...
Washegari kuma a Somalia, wannan yaron ya leko kansa a bargo bayan an fesa maganin hana kamuwa da cutar korona a sansanin 'yan gudun hijira a Mogadishu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Washegari kuma a Somalia, wannan yaron ya leko kansa a bargo bayan an fesa maganin hana kamuwa da cutar korona a sansanin 'yan gudun hijira a Mogadishu.
Mutum biyu suna boksin

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ranar Juma'a, lauya Shadrack Wambui yana atisaye a Nairobi, Kenya, inda yake horas da 'yan damben boksin da kuma bayar da shawarari kan sha'anin sharia'a
Mutane biyu suna dasa bishiya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kwana biyu bayan haka, masu aikin sa-kai suna dasa irin bishiya a gefen Kogin Nairobi. Mambobin kungyar Canaane Riverside Green Peace sun dasa bishiyoyi 500 a shekaru biyu da suka wuce kuma suna kwashe dattin gefen tekun a duk karshen mako.
Ma'aikatan kashe gobara suna wucewa ta cikin ɓaraguzai bayan gobarar da ta lakume Dakin Karatu na Jagger a Jami'ar Cape Town a Afirka ta Kudu, inda aka adana bayanai kan Nazari game da Tarihin Afirka.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ma'aikatan kashe gobara suna wucewa ta cikin ɓaraguzai bayan gobarar da ta lakume Dakin Karatu na Jagger a Jami'ar Cape Town a Afirka ta Kudu, inda aka adana bayanai kan Nazari game da Tarihin Afirka.
A ranar ce wadannan iyalan da ke wajen Luanda babban birnin Angola, suna zaune kofar gidansu bayan ruwan da aka kwashe lokaci ana yi kamar da bakin kwarya da ambaliyar ruwa da suka yi sanadin mutuwar akalla mutum 24 sannan suka lalata gidaje 60

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar ce wadannan iyalan da ke wajen Luanda babban birnin Angola, suna zaune kofar gidansu bayan ruwan da aka kwashe lokaci ana yi kamar da bakin kwarya da ambaliyar ruwa da suka yi sanadin mutuwar akalla mutum 24 sannan suka lalata gidaje 60
Ranar Asabar a Kamaru, an binne Cardinal Christian Tumi. An yaba wa archbishop din mai shekara 90 wanda ba ya shayin bayyana ra'ayinsa bisa yunkurin da ya yi na yin sulhu tsakanin hukumomi da 'yan a-waren kasar. Fafaroma Francis ya ce "ya yi tasirin da ba za a manta da shi ba a Coci da kuma rayuwaryau da kullum da siyasar" Kamaru.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Asabar a Kamaru, an binne Cardinal Christian Tumi. An yaba wa archbishop din mai shekara 90 wanda ba ya shayin bayyana ra'ayinsa bisa yunkurin da ya yi na yin sulhu tsakanin hukumomi da 'yan a-waren kasar. Fafaroma Francis ya ce "ya yi tasirin da ba za a manta da shi ba a Coci da kuma rayuwaryau da kullum da siyasar" Kamaru.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka