Najeriya: Kayan gwari sun yi kwantai a arewa bayan hana kai kaya kudu

A yayin da farashin kayan gwari da dabbobi suka tashi a kudancin Najeriya, a arewacin kuma farashin kayayyakin ne ya karye.
Tasirin yajin aikin Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu kayan gwari da dabbobi da kayan cimaka ya haifar da tashin farashin a kudancin Najeriya da kuma karyewar farashin a arewacin ƙasar.
Ƴan kasuwar kayan gwari a Kano sun yi kukan faɗuwar farashin tare da tabka asara mai yawa.
Akwai tarin tumatus kwando-kwando jibge a kasuwar kayan gwari a Kano bayan hana kai kayan zuwa kudancin Najeriya.
Kusan ana kai kayan gwari kashi 50 waɗanda aka noma a yankin arewaci zuwa kudancin Najeriya, kuma yanzu rashin kai kayayyakin ya haifar da yawaitarsu a arewa wanda ya jefa ƴan kasuwar kayan gwari cikin wani yanayi na hasara.
Tun a makon jiya ne ƴan kasuwar da ke kai kayan abinci kudancin Najeriya daga yankin arewaci suka shiga yajin aikin kafin su janye a ranar Laraba.
Ƙungiyar ta janye yajin aikin ne bayan tattaunawa da tawagar gwamnatin tarayya karkahin jagorancin gwamnan jihar Kogi.
Ƙungiyar ta ce ta mika bukatu guda biyar ga gwamnan domin gabatar da su ga shugaban ƙasa da take son a biya mata.
Ta amince ta janye yajin aikin bayan gwamnati ta yi alkawalin diba bukatun, amma kungiyar ta yi barazanar komawa yajin aikin idan har gwamnati ba biya bukatun ba.
Sun shiga yajin aikin ne domin nuna goyon baya ga ƴan uwansu mutanen arewa da rikicin kasuwar Sasa ya shafa a garin Ibadan na jihar Oyo, rikicin da ya haifar da hasarar rayuka.
Yanzu yajin aikin ya yi tasiri bayan haifar da tsadar farashin kayayyakin abinci a yankin kudu maso yammacin Najeriya da kuma faɗuwarsa a arewaci.
Hakan ya nuna yadda yankunan biyu na Najeriya ke dogaro da juna.
Rahotanni sun ce shugabannin ƙungiyar kayan gwarin sun yi zama da wakilan gwamnatin tarayya a fadar shugaban ƙasa domin janye yajin aikin.
Farashin kayan gwari a arewa

Ƴan kasuwar kayan gwari a Kano sun ce rashin kwararowar abokan cinikayyars na yau da kullum ya sa kayan da suke da su lalacewa wanda hakan ya sa dole su karye farashin kayayyakin don gudun tafka asara.
A kudancin Najeriya kuma farashin ya lunka sau uku sakamakon yajin aikin.
Wakilin BBC Kalipha Shehu Dokaji ya ziyarci kasuwar kayan gwari ta Yankaba a Kano ya ce ya tarar da yadda farashin kayan gwarin ya karye.
Ya ce yanzu a kasuwar ana sayar da kwandon tumatur naira 1,000 saɓanin dubu uku zuwa huɗu da ake sayarwa kafin yajin aikin na masu kai kayan gwari zuwa kudancin Najeriya.
Wasu wuraren ma idan mutum ya latsa har ƙasa da naira 500 za a iya sayar masa da kwandon tumaturin.
Kwanon tumatur da ake sayarwa naira 800 yanzu ya koma 200, haka ma kwanon tattasai ya koma 200 saɓanin narai 1,200.
Buhun albasa anzu ya dawo naira 500 maimakon dubu 65 kafin soma yajin aikin na masu kayan gwari.
Ƴan kasuwar sun alaƙatanta asarar da suka yi da ƙaranci shigowar masu siyen kayan da yajin aikin da mutanensu da ke fataucin kayan zuwa kudu.
Asarar ta fi shafar ƴan tumatur, yayin da kuma masu cefene ke murna da karyewar farashin.
Sai dai duk da wannan matsalar karyewar farashi da yan kasuwar da wasu daga cikin manoman ke kokawa, wasunsun sun shaida wa BBC cewa sun gwamance da hakan domin goyon bayan yajin da masu dakon kayan zuwa kudancin Najeriya ke yi.
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu dakon abinci da dabbobi daga arewa zuwa kudancin Najeriya sun shiga yajin aikin ne bayan karewar wa'adi da ta bai wa hukumomin Kasar na biya masu wasu bukatunsu musamman kan rkicin kasuwar Shasha a jihar Oyo.











