Yanayi a Ingila: Hotunan yadda dusar ƙanƙara ke kawo cikas ga mazauna Birtaniya

James Ring uses a surf board to sledge down a snow covered hill in Wye National Nature Reserve near Ashford in Kent

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, An yi ta zubar dusar ƙanƙara a Kent a kwanakin ƙarshen makon da ya gabata
An wallafa

Zubar ƙanƙara mai tsanani ya kawo cikas ga al'amura da dama a wasu yankunann Birtaniya, al'amarin da ya sa aka rufe cibiyoyin da ake yin allurar riga-kafi sannan aka rufe makarantu a wasu yankunan.

Dama an fitar da gargaɗn cewa za a samu zubar ƙanƙara mai tsanani a Landan da kudu maso gabshin Ingila da Nottinghamshire da Sheffield da kuma Lincolnshire.

Ƴan sanda sun yi wa mutane gargaɗi cewa kada su yi tafiye-tafiye, don ana sa ran za a samu tsaiko.

A Landan da kuma kudu maso gabas, ana sa rana santimita 5 zuwa 10 na dusar ƙanƙara ce za ta zuba.

Abandoned cars in a snow filled ditch in Needham Market in Suffolk

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Wasu mooci da suka ƙafe a cikin dusar ƙanƙara a Suffolk ranar Litinin
A snowplough clearing the road near Barham, Ipswich

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Ana aikin kawar da ƙanƙarar daga titi a Ipswich
A skier makes their way through the snow in Wye National Nature Reserve near Ashford in Kent on Sunday

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Masu wasan zamiya sun ji daɗin zubar ƙanƙarar a ranar Lahadi a Kent
A vaccination centre at the Jobserve Community Stadium in Colchester, which was forced to close on Sunday because of the weather

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, An rufe wata cibiyar yin allurar riga-kafin cutar korona Colchester ranar Lahadi saboda munin yanayin
A car navigates in snow near Bradfield Dale, South Yorkshire

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Motoci kan ƙafe a cikin dusar
Burgh in Suffolk

Asalin hoton, victorthevole/BBC Weather Watchers

Bayanan hoto, Masu ɗaukar hoto na BBC da ke bibiyar yanayi sun yi ta ɗaukar hotuna kamar wannan a Suffolk
River Eden in the town of Cupar, in Fife, Scotland having burst its banks.

Asalin hoton, @shamblesklutz/PA Media

Bayanan hoto, Daga baya a wasu sassan ƙanƙarar ta narke ta zama tamkar ruwan ambaliya ta yadda sai an yi amfani da kwalw-kwale
Snow covers Moulin Moor near Pitlochry as storm Darcy approaches the country, in Scotland

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dusar ƙanƙara ta rufe yankin Moulin Moor a Perthshire