Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yanayi a Ingila: Hotunan yadda dusar ƙanƙara ke kawo cikas ga mazauna Birtaniya
An wallafa
Zubar ƙanƙara mai tsanani ya kawo cikas ga al'amura da dama a wasu yankunann Birtaniya, al'amarin da ya sa aka rufe cibiyoyin da ake yin allurar riga-kafi sannan aka rufe makarantu a wasu yankunan.
Dama an fitar da gargaɗn cewa za a samu zubar ƙanƙara mai tsanani a Landan da kudu maso gabshin Ingila da Nottinghamshire da Sheffield da kuma Lincolnshire.
Ƴan sanda sun yi wa mutane gargaɗi cewa kada su yi tafiye-tafiye, don ana sa ran za a samu tsaiko.
A Landan da kuma kudu maso gabas, ana sa rana santimita 5 zuwa 10 na dusar ƙanƙara ce za ta zuba.