'Ƴan sanda sun tambaye ni ko mijina maye ne ina tsaka da alhinin mutuwarsa'

    • Marubuci, Daga Roncliffe Odit da Basillioh Mutahi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Swahili, Nairobi
  • An wallafa

A lokacin da Chirindo Chisubi ke tsaka da alhinin mutuwar mijinta, ta yi mamakin tambayar da ƴan sanda masu bincike kan mutuwar tasa suka yi mata a lardin Kilifi da ke Kenya.

"Wannan mutumin, mai gidanki yana tsafi?" suka tambayi matar mai shekara 63.

Mijinta, Dzuya Chisubi, an kashe shi ne bisa zargin yana tsafi ko maita.

Chirindo ta san mijinta bai taɓa yin tsafi ba kuma ta yi imanin cewa an kashe shi ne bisa wani dalili na daban - a kan rikicin wani fili.

"Na shaida wa ƴan sanda cewa tun da na aure shi ban taɓa ganin wata alama a tattare da shi mai nuna yana tsafi ba," a cewarta.

Mutuwar mijin nata ta yi mata ciwo, duk da cewa babu abin da za ta iya yi a kai.

An shaida mata cewa ɗan uwan mijinta ne ya shirya kisan, kamar yadda ta shaida wa BBC, inda ta ce mutumin da aka ɗauka ya yi kisan ne ya gaya wa ƴan sanda da kansa.

An kama mutanen biyu kuma an gurfanar da su. Su duka biyun sun musanta zargin.

Ƙaburbura da yawa a ƙauyen

Takaicin da Misis Chisubi ke ciki ba sabon abu ba ne ga mazauna yankin Buni Kisimali a Kifili, inda suke shiga mawuyacin hali saboda yarda da ake yi da maita.

Akwai ƙaburbura da dama a ƙauyen, da yawa an kashe mutanen ne ta muguwar hanya.

A wannan yankin ba abin mamaki ba ne idan iftila'i ya sauka a gari kamar cuta ko yawan mutuwa a ce maita ce.

Sau da yawa, ana zargin maza tsofaffi da aikata maita sannan ana ba su laifi idan waɗannan abubuwan sun faru. Wani lokaci kisa ne hukuncin da ake yanke masu.

Sai a sassare su ko a ƙona su ƙurmus har su mutu.

Wasu ma danginsu ne ke kashe su.

Mutane a nan na rayuwa ne bisa dokokin al'ada da addinan Musulunci ko na Kirista, waɗanda su ne addinan da suka fi shahara a Kenya.

Wani bincike da Cibiyar Pew Research Centre ta gudanar a 2010, ya gano cewa kashi 11 cikin 100 na ƴan Kenya sun yarda da maita.

Gwamnati ba ta tara bayanai kan yawan masu yarda da maita, wanda doka ba ta amince da shi ba kuma a kan ɗaure waɗanda aka kama da laifinsa tsawon shekara 10 a gidan kaso, amma kafofin yada labarai na ƙasar na yawan yin rahotanni kan masu aikata maita a ƙasar.

Rahotonni kan ƙunshi kashe waɗanda ake zargi da maitar.

Ƴan sanda sun shaida wa BBC cewa a lardin Kilifi kawai, an kashe sama da maza tsoffi 150 a shekaru biyun da suka gabata bisa zargin aikata maita.

'Ana zargin juna'

Tsoffi maza da mata a ƙauyen Buni Kisimani na zaman ɗar-ɗar.

Lokacin da BBC ta isa ƙauyen a bara, akwai maza matasa da yawa, wasu a kan babura, wanda su ne hanyoyin sufuri da suka fi shahara a yankin.

Ba a cika ganin maza tsofaffi ba.

Babu mamaki, ambaton sunan wani tsoho na iya jefa mutane cikin fargaba.

Alaƙanta tsoffi da maita na janyo tsoro tsakanin wani ɓangare na al'umma.

Amma tsoffin da wasu danginsu na zaman fargabar cewa ana iya kai masu hari saboda yarda da maita.

Ɗan gaba kaɗan daga ƙabarin Mista Chisubi a ƙauyen, akwai wani ƙabarin - na mahaifin Mwakoyo Dzayo wanda aka kashe bara.

Mista Dzayo ya ce an kashe mahaifinsane kan zargin shi boka ne, zargin da ya musanta.

"Ban taɓa ganinsa, ko da rana ɗaya, yana bokanci ba," a cewarsa.

Me ake yi a kai?

Hukumomi sun ce sun kama mutum 28 bisa kisan tsoffin maza 10 a yankin.

Sai dai, ɓarkewar annobar cutar korona ta janyo tsaiko a wasu shari'o'in, ciki har da ta Mista Chisubi, wadda ya kamata a yi zaman saurarenta a watan Fabrairu.

Khamisi Mwaguzo, mai kula da shirin Musulmi matasa ta Kenya Muslim Youth Alliance, ya ce yana ci gaba da bincike kan wannan lamari - ya kuma ce ya kamata kowa ya sa hannu a batun.

Ya bayyana cewa ɓangarori da dama na al'umma sun daɗe suna zargin juna bisa matsalolin da ke faruwa saboda bambancin addini da al'ada.

Yana kawo waɗanann ɓangarori wuri guda don ilimantar da su da shirya tsakaninsu.

"Wasu daga cikin Kiristocin na cewa shugabannin gargajiya mugaye ne, wai ba su da wayewar kai.

"Ƴan gargajiyar kuma na cewa masu bin addinai su ne suka jawo kashe tsoffi da ake yi," a cewarsa.

Mista Mwazugo ya ce dole ne duka ɓangarorin ciki har da Musulmi da Kirista da 'Yan gargajiya su haɗa kai su koya wa mazauna yankin su fahimci babu maita a nan".

"Dole ne matasa su koyi hanyoyin dogaro da kansu kawai maimakon dogara da gonakin iyayensu da suka manyanta," in ji shi.

'Rikicin Fili'

Shekara guda kenan da kisan mijin Misis Chisubi, kuma tana fatan za a yi mata adalci.

Ba ta yarda an kashe mijinta saboda zargin maita ba ne, illa rikicin gadon fili da yake yi da ɗan uwansa.

Suna da wata gona ta mahaifinsu, abin da ya rage kawai a samu wanda zai raba masu ita," a cewarta.

Shugaban ƴan sanda a Rabai, Fred Abuga ya ce rikicin fili da son zuciya na son yin arziki cikin gaggawa su ne kan gaba wajen haifar da yawan kashe-kashe a yankin, kamar yadda bincikensu ya gano.

"Tushen waɗannan matsalolin shi ne fili. Sai ka ga maza tsoffi da dama na da takardun filayensu.

"Matasan ne da ba su shiga harkar fili za ka ga ba su da filaye kuma ba su da wata sahihiyar hanyar samun kuɗi, mafi yawansu ne ke aikaTA waɗannan laifukan," a cewarsa.

'Ba mu kuɓuta ba'

Duk da yunƙurin da ake ta yi na son ganin an shawo kan matsalar, ba a daina kashe-kashen ba.

"Yanzu da muke magana, ɗaya daga cikin manyanmu na ƙabilar Kaya Chonyi na can a kwance a mutuware," a cewar Daniel Mwawara Garero, shugaban majalisar dattawa ta yankin.

"Ko a daya daga cikin unguwannin a nan, akwai wani dattijo da aka yanka rannan, don haka ba a daina kisan ba, kuma muna rayuwa cikin tsoro," ya ce

Ko iyalin Misis Chisubi na cikin fargabar abin da ya faru tun mutuwar mijinta.

"Yanzu yana fushi da ƴaƴana, ta ce, game da ƙanin mijinta da aka saki daga hannun ƴan sanda bayan da ya musanta zargin da ake yi masa a kotu.

Mutumin da ya amsa laifin na can a gidan kaso yana sauraren shari'a.

"An ce mu tashi daga gidanmu saboda mun fiye surutu kuma mu ba mu san me ake nufi da haka ba.

"Ba mu muka kai ƙararsa wurin ƴan sanda ba, shi wanda ya yi kisan shi ya kai ƙarar.

"Ba mu kuɓuta ba, ba ma cikin farin ciki kwata-kwata," a cewarta.