Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Son, Ramos, Zaha, Ibrahimovic, Ndombele

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Tottenham Jose Mourinho ya yi amanna cewa sabunta kwantiragin Son Heung-min, dan wasan kungiyar mai shekara 28, wanda wa'adinta zai kare a 2023, ma bukatar hakuri da dabara. (Evening Standard)
Raunin da dan wasan baya na kasar Spaniya Sergio Ramos ya ke fama da shi na iya jano jinkirin sabunta kwantiraginsa a Real Madrid har zuwa lokacin da ya warke, inda wa'adin dan wasan mai shekara 34 za ta kawo karshe a karshen wannan kakar wasan. (Marca)
Kocin Crystal Palace Roy Hodgson na sa ran kungiyarsa ta dauko Wilfried Zaha a karshen wannan kakar wasan, ganin cewa dan wasan mai shekara 28 kuma dan kasar Ivory Coast na sha'awar buga wasannin gasr Zakarun Turai. (Mail)
Manajan AC Milan Stefano Pioli ya ce ya dace a ce Zlatan Ibrahimovic, dan wasan gaba mai shekara 39 ya ci gaba da buga wasanni tare da kungiyar ta Italiya. Wa'adin dan wasan mai shekara 34 za ta kawo karshe a karshen wannan kakar wasan. (Sky Sports Italia, via Football Italia)
Shugaban sashen kwallo na Ajax Marc Overmars ya kusa sauka daga mukamin a karshen wannan kakar wasan, inda a ke hasashen zai iya komawa tsohuwar kungiyarsa Barcelona ko Arsenal. (Mundo Deportivo)
Dan wasan tsakiya na Faransa Tanguy Ndombele mai shekara 24 ya yarda cewa dole ya sauya salon wasansa idan yana son samun nasarori a Tottenham. (Telegraph - subscription required)
Dan wasan Chelsea da Jamus Timo Werner mai shekara 24 bai iya zura kwallo ko daya ba a wasanni 14 da ya buga a gasar firimiyar Ingila. Amma ya ce ya yi imani lokaci na zuwa da zai koma ganiyarsa (Evening Standard)
Tsohon alkalin wasan gasar firimiya Mark Halsey ya ce amfani da fasahar VAR na kawo sauye-sauye saboda zamani, amma ya ce "tilas a tausaya wa alkalan wasan wadanda sun kusa kasa wa saboda gajiya". (Sun)









