Kurakuren da Manchester United ta yi a wasa da Everton

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta buga 3-3 da Everton a wasan mako na 22 a gasar Premier League da suka kara a Old Trafford ranar Asabar.
United ce ta fara zura kwallo biyu ta hannun Edinson Cavani da kuma Bruno Fernandes, yayin da Eveton ta farke ta hannun Abdoulaye Doucoure da kuma James Rodriguez.
Saura minti 20 a tashi daga karawar United ta kana na uku ta hannun Scott McTominay, sai dai daf da za a tashi Dominic Calvert-Lewin ya farkewa Eveton.
Wannan ne wasa na uku da suka kara a tsakaninsu a bana, inda United ta yi nasara a karawar farko a Premier da ci 3-1 a Goodison Park cikin watan Oktoba.
United ta kara doke Everton har gida da ci 2-0 a FA Cup da suka fafata cikin watan Disamba.
Wannan ne wasa na hudu da United kan yi a gida ta zura kwallo a raga a kalla biyu, amma a farke ta kasa yin nasara.
An ci United kwallo 18 a fafatawa 12 da ta yi a Old Trafford a gida a bana, bayan da a bara 19 suka shiga ragarta.
Everton ta ci kwallayenta uku a dukkan hare-haren da ta kai, ita kuwa United ta ci nata ne daga hari biyar da ta yi.
United za ta karbi bakuncin West Ham United ranar Talata a FA Cup, daga nan ta ziyarci West Brom a gasar Premier League ranar 14 ga watan Fabrairu.
Ita kuwa Everton za ta karbi bakuncin Tottenham a gasar FA Cup ranar Laraba, sai kuma Fulham ta ziyarci Goodison Park ranar Lahadi.









