Zababbun hotunan Afirka na mako: 29 ga Janairu zuwa 4 ga Fabrairun 2021

An wallafa

Ga wasu zaɓaɓɓun hotun da aka ɗauka a nahiyar Afirka ko na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya a wannan makon:

A man in a yellow rain coat walks past a brightly coloured mural.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mutum yana tafiya sanye da rigar ruwa a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu a ranar Talata.
A boy looks through a gap in a fence.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kafin wannan ranar, wani yaro ne yake leƙe daga cikin sansanin ƴan gudun hijira a yankin Darfur na Sudan.
An athlete jumps on a racetrack.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ɗan wasan tseren Sudan Ta Kudu Akoon Akoon yana atisaye a filin tsere a Japan gabanin Gasar Olympic ta Tokyo 2020 Olympic Games, wacce aka jinkirta ta da shekara saboda annoba.
Muslim women wearing hijabs smile and pose for selfies.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Litinin, waɗan nan matan sun ci ado suna ɗaukar hoto don murnar bikin Ranar Hijabi Ta Duniya a Monrovia, babban birnin Laberiya.
Traditional soap called Cabacourou.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan kuwa sabulun gargajiya ne ɗan ƙasar Ivory Coast da aka yi da manja wanda ake kira Cabacourou, ake aikin mulmula shi a ranar Litinin.
Student stand in a line durign a graduation ceremony.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ɗaliban Stella Maris Polytechnic a Monrovia sun yi layi a yayin bikin kammala karatunsu a ranar Juma'a.
A Tunisian woman carrying a dog gestures with her middle finger as she faces police officers forming a human shield to block the access to demonstrators to the interior ministry.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Washe gari kuma a Tunis babban birnin ƙasar Tunusiya, mutane ne suka bazu a kan tituna suna zanga-zangar rashin samun ayyukan yi da kuma cin zarafin da ƴan sanda ke yi wa mutane.
A man points to names etched on a memorial.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba, wani ɗan Uganda Olanyia Mohammed mai shekara 38 da ya tsere wa kisan kiyashin da ƙungiyar Lord's Resistance Army suka yi a Lukodi a 2004, yana nuna sunayen mahaifansa a jerin sunayen da aka wallafa na wadanda suka mutu. A ranar Alhamis ne aka yanke wa kwamandan ƴan tawaye Dominic Ongwen, wanda ya kitsa harin da sauran mabiyansa, hukunci kan laifukan yaƙi.
Workers harvest grapes at the La Motte wine farm in Franschhoek near Cape Town.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kuma a ranar Juma'a, wasu ma'aikata na girbe inibi a wata gona a Afirka ta Kudu.

Dukkan hotunan suna da haƙƙn mallaka.