Riga-kafin Covid -19: Masu aiki da wadanda ke kan hanya

Scientist with syringe and bottle marked "Covid 19"

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

A sassan duniya daban-daban, ana ta koƙarin yi wa al'umomi alluran riga-kafin cutar korona.

Akwai wasu jerin alluran riga-kafin da aka samar ta hanyoyin bincike mabanbanta, kuma ana amfani da su ne domin rage yawan mace-mace da kamuwa da cutar, har ma da rage yawan waɗanda ake kwantarwa a asibitoci.

An kuma sanar da duniya cewa an yi nasarra samar da wasu sabbin alluran riga-kafi cikin makon nan - alluran da aka tabbatar su na da tasiri kan kusan duka nau'in kwayar cutar ta korona.

Abin da ya sa duniya ke buƙatar riga-kafi

Fiye da shekara guda ta wuce tun da annobar korona ta bayyana, amma har yanzu yawancin mutane na cikin hatsarin harbuwa da kwayar cutar.

Matakan killacewa da bayar da tazara da kuma sanya takunkumi su ne kawai ke kare mu daga kamuwa da cutar ta Covid-19.

Riga-kafi kuwa shi ke koya wa jikin ɗan Adam yadda zai yaƙi cutar da zarar ta shiga jikinsa.

Manyan kamfanoni uku

A halin yanzu, akwai kamfanoni uku da ke kan gaba wajen samar da riga-kafin annobar ta korona: Pfizer/BioNTech da Moderna da kuma Oxford/AstraZeneca.

Kamfanonin Pfizer da Moderna suna da tsari iri ɗaya ne.

Riga-kafin da su ka samar ana yin allurar wani ɓangare na kwayar cutar ne a jikin ɗan Adam, wanda daga nan ke sa jikin ya samar da wasu kwayoyin halitta da za su kare jikin daga harin da aka kai ma sa.

An amince da fara amfani da su a Birtaniya da Turai da kuma Amurka.

Amma riga-kafin da jami'ar Oxford ta samar ya bambanta da sauran domin yana amfani ne da wani sinadari maras cutarwa domin samar da kariyar da jikin ke bukata.

An amince da amfani da shi a Birtaniya da Turai.

Ina labarin sababbin alluran?

An kuma samar da wasu sabbin allura riga-kafin a ƙarshen watan nan na Janairu.

Kamfanonin Janssen da Novavax su ka fitar da sabbin alluran, waɗanda za a tantance su kafin a bayar da amincewar fara amfani da su.

Presentational grey line

Me sauran ƙasashe ke yi?

Ban da waɗannan, akwai wasu fitattun alluran riga-kafin da wasu ƙasashen ke haɗa wa.

Sai dai ba a amince da amfani da su a Turai da Amurka ba.

Akwai Sinovac da CanSino da Sinopharm. Dukkansu daga China su ka fito, kuma ta kulla yarjejeniya da wasu ƙasashe na Asiya da Kudancin Amurka.

Akwai rahotannin da ke cewa tuni an yi wa mutum miliyan ɗaya allurar riga-kafin Sinopharm a cikin China.

Akwai kuma Sputnik V wanda Rasha ta samar a cibiyar bincike na Gamaleya Research Centre wadda ta wallafa alkaluman sakamakon gwajin da ta yi - kuma ya tabbatar cewa wasu mutanen da aka yi gwaje-gwajen a jikinsu sun sami kariya daga kamuwa da cutar korona.