Palestine: Biden zai dawo da tallafin da Amurka ke bai wa Falasɗinawa

Biden da Abbas

Asalin hoton, AFP

An wallafa

Sabon wakilin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ya ce gwamnatin Shugaba Biden na da niyyar dawo da tallafi ga Falasdinawa, wanda Shugaba Trump ya soke.

Yayin da yake jawabi ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, Richard Mills ya ce Amurka za ta ci gaba da rokon karin kasashen Musulmi da su daidaita alakar su da Isra'ila.

Amma ya ce wannan ba zai maye gurbin zaman lafiyar Isra'ila da Falasdinu ba.

Tawagar Shugaba Trump ta shawo kan kasashe da dama ciki har da UAE da Bahrain da su kulla alaka da Isra'ila.

Sai dai an riƙa kallon kokarin da ya yi na cimma yarjejeniyar da za ta warware rikicin Isra'ila da Falasdinu a matsayin son rai, saboda yadda tafi zama riba da Isra'ila.

Ita dai gwamnatin tsohon shugaban Amurka Donald Trump ta ɗauki matakai da dama kan rikicin Falasɗinawa da Isra'ila, da ake ganin sun taimaka wajen ƙara dagulewar yiwuwar cimma zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin ƙasashen biyu.

Ya ce gwamnatinsa ce ta fi dacewa ta sasanta dadaddiyar takaddamar da ke tsakanin Falasdinawa da Isra'ila.

Ya taɓa kama sunan shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas karara, yana cewa: "Ka sani idan kuka rungumi sasanci da zaman lafiya kasashen duniya za su so ku sannan za su mara maku baya domin ci gaban kasarku."

"Abin kasarku ke samarwa zai ninka sannan tattalin arzikinku ya hauhawa... babu wanda za a raba da muhallinsa tsakanin Falasdinawa da Yahudawa."

Wani mataki da tsohon shugaban ya ɗauka shine na ayyana birnin Ƙudus a matsayin na Isra'ila, yana cewa "zai ci gaba da zama babban birnin Isra'ila halak malak".