'Adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya ya ragu da fiye da miliyan 3'

An wallafa

Gwamnatin Najeriya ta ce adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a ƙasar ya ragu da fiye da yara miliyan uku, sakamakon duƙufar da ta yi wajen wayar da kan iyaye da ba da tallafi.

Ministan ilimin Najeriya, Mallam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan inda ya ce yawan yaran da ba sa zuwa makaranta ya ragu daga mutum miliyan goma da dubu ɗari zuwa miliyan shida da dubu ɗari tara da ɗoriya, duka-duka a cikin shekara ɗaya da rabi.

Wannan nasarar, kamar yadda ya ce, ta samu ne ta hanyoyi daban-daban da ma`aikatar ta bi don kwaɗaita wa yara da iyayensu karatun zamani, musamman ma wayar da kan su a kan muhimmancin ilimi.

Mista Ben Goong, shi ne kakakin ma`aikatar ilimin, kuma cewa ya yi, gwamnatin tarayya ta samu kayan tallafa wa karatu da kwaɗaita wa yara da iyaye da ya kai dala miliyan ɗari shida daga bankin duniya, wanda ta rarraba wa jihohi a ƙarƙashin wani shiri da aka yi wa laƙabi da shirin samar da ilimi mai inganci ga kowa.

"Mun ƙaddamar a jihohi goma ne, amma yanzu jihohi goma sha bakwai ne a cikin shirin," in ji shi.

"Kuma babban abin da muke yi shi ne shigar da gwamnoni da sarakunan gargajiya da malaman addini da sauran masu faɗa-a-ji, da kuma masu mkarantun kuɗi a cikin aikin wayar da kan jama`a a kan muhimmancin karatun yara.

"Kuma tuni muka miƙa kason farko na kuɗin ga dukkan jihohi," in ji shi.

Wannan salo ko tsari, kamar yadda ma`aikatar ilimin Najeriyar ke cewa, ya samu karɓuwa, kuma yana tasiri sosai wajen kwaɗaita wa yara shiga makaranta.

Kuma ganin yadda ake samun nasara, gwamnatin Najeriyar na sa ran cewa nan ba da daɗewa ba yara ƙalilan ne da za su rage suna gararamba ba sa zuwa makaranta.

Mista Goong ya ƙara da cewa "Muna sa ran cewa adadin yaran da ba sa zuwa makaranta zai dinga raguwa. Bayan haka, mun fahimci cewa iyayen da suka yi karatu ba sa sakaci, suna sanya `ya`yansu a makaranta. Saboda haka, ministan ilimi ya ce za mu jefi tsuntsu biyu da dutse daya.

"Za mu yi ƙoƙarin koyar da iyayen yara yaƙi da jahilci ta yadda ba za su yi wasa wajen tura `ya`yansu makaranta ba," in ji shi.

Ma`aikatar ilimin Najeriyar ta ce adadin yaran da suka shiga makaranta a shekarar da ta wuce ya zarta ainihin adadin da ta yi hari da mutum aƙalla miliyan uku.

Kuma wannan ya ƙara wa gwamnatin Najeriyar kwarin-gwiwa cewa nan ba daɗewa ba za ta fita daga sahun ƙasashen da ke gaba wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya.