Yadda lalacewar makarantu ke cikas ga ilimin boko a Kano

Makarantu da dama sun lalace a cikin kauyuka
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Daya daga cikin matsalolin da ke damun ilimi a Najeriya shi ne lalacewar makarantu, wato gine-ginen da ake amfani da su wajen koyar da yara karatu.

Arewacin Najeriya, shi ne yankin da ya fi yawan yara da ba su zuwa makaranta a Najeriya. Sai dai jihohin da dama suna daukan matakan ganin sun rage matsalar ta hanyar samar da dokoki wadanda ke tilasta wa iyaye sanya yaransu makaranta.

Kano na daya daga cikin jihohin da suka dauki wannan mataki, inda a watan Nuwamba na shekara ta 2020 gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan dokar tilasta wa yara samun ilimi kyauta a jihar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Sai dai daya daga cikin matsalolin da ake ganin za su yi zagon kasa ga wannan doka shi ne rashin kyakkyawan muhalli na koyarwa.

Gwamnatin Kano ta amince da dokar tilasta wa yara zuwa makaranta

Asalin hoton, FACEBOOK/KANO MIN OF EDU

Duk da kuwa cewa kwamishinan ilimi na jihar Muhammad Sanusi Kiru ya shaida wa BBC cewa jihar ce a sahun gaba wurin kashe wa ilimi kudi a fadin Najeriya.

Ya shaida wa BBC cewa a karshen shekara 2020 an bai wa kowace karamar hukuma ta jihar kudi Naira miliyan 20 domin ta gudanar da aikin gyaran azuzuwa a makarantun firamaren gwamnati.

Wannan a cewarsa kari ne a kan kujerun zama da gwamnatin ta raba a daukacin makarantun jihar.

Haka nan ya ce gwamnatin ta fitar da kudi Naira miliyan dubu daya da dari biyar ta hada da wata Naira miliyan dubu daya da dari biyar domin aikin gina azuzuwa, da kuma samar da sabbin makarantu.

Kusan dukkanin azuzuwan wannan makaranta dalibai na zama ne a kasa

Sai dai BBC ta zagaya wasu daga cikin makarantu a yankunan karkara na jihar domin ganin yadda yanayin makarantun firamaren na gwamnati suke.

A wani kauye da ke karamar hukumar Dawakin Kudu daukacin azuzuwan ba su a cikin yanayi mai kyau.

Makaranta ce da ke a farkon shiga kauyen, ba ta da katanga balle a yi maganar kofar da za a iya kullewa domin hana yara shiga a lokacin da ba a karatu.

Aji 6 na wata makarantar firamare a karamar hukumar Dawakin Kudu

Akasarin azuzuwan babu kujerun zama na dalibai, sannan siminti ya farfashe.

Wasu azuzuwan rufinsu ya farfashe, babu murfin kofa, kuma babu murafen tagogi.

Wasu mutanen kauyen da BBC ta tattauna da su sun ce yanayin makarantar na damun su.

Al'umma na kokawa saboda rashin kulawar gwamnati wurin gyara makarantu

Wani mutum mai suna Aminu Idris wanda yaronsa dalibi ne a makarantar ya ce "Gaskiya muna jin abin ba dadi domin kuwa yaranmu sukan zo makaranta da inifom din su amma dole sai sun yi wanki duk bayan kwana daya ko biyu, kayan makarantar ba su dadewa saboda yawan wanki a kullum. Babu abin zama kuma kasan babu dabe."

Mallam Mato "Abu duk ya tabarbare, kuma wannan rashin kyawu na makarantar nan ya dade a haka, amma tunda muna son ilimin ya za mu yi, ko a rami ne haka za mu tura su."

A wani kauyen kuma na daban da BBC ta kai ziyara ta ga yadda rufin gini ya rufta cikin azuzuwa, abin da ya sanya da alamu aka daina amfani da azuzuwan guda biyu, a makarantar wadda ke da azuzuwa hudu.

Yawancin makarantu babu bandaki mai tsafta

Sauran azuzuwa biyu da suka rage kuma ba su da murafen kofa da na taga, kuma yara ne ke shiga suna wasan kwallon kafa.

Rashin kofofi da tagogi dai ya sa yara na shiga ajjujuwan suna yin kwallon kafa.

Iyaye sun damu matuka sanadiyyar rashin kyawun makarantu

A gefen ajujuwan guda hudu na wannan makarantar na ga wata runfa wadda da alama an yi ta ne a matsayin wurin ajiye ababen hawa, amma yaran da na iske sun shaida min cewa nan ma wani aji ne da ake koyar da dalibai.

Kano ce jiha mafi yawan al'umma a Najeriya

Mutane da dama wadanda BBC ta tattauna da su a wadannan kauyuka sun ce sun cire tsammani yaransu za su samu wani ilimi mai inganci a nan kusa, duk kuwa da cewa sau da dama sun sha yin nasu bakin kokarin wajen ganin sun magance wasu matsaloli da makarantun fama da su.

Wannan rahoto ne na musamman da BBC Hausa ta kawo maku tare da tallafin gidauniyar MacArthur.