Zamfara: Dalilin da ya sa muka ƙwace lasisin duka makarantu masu zaman - Gwamnatin jihar

..

Asalin hoton, @Bellomatawalle1

An wallafa

Gwamnatin jihar Zamfara, ta ce ta soke lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu da ke faɗin jihar har sai ta kammala tantance su.

Ta ce ta ɗauki matakin ne don bai wa masu irin waɗannan makarantu damar neman izinin ci gaba da aiki bisa yadda doka ta tanada.

A cewarta, ɗaukar matakin ya zama tilas, ganin yadda mutane ke buɗe makarantu kara-zube da kuma gudanar da harkokin ilimi cikin yanayin da ya gaza mizani mafi ƙaranci da ma'aikatar ilimi ta tarayya ta shimfiɗa.

A wata hira da BBC, kwamishinan ilimi na jihar ta Zamfara Ibrahim Abdullahi Gusau, ya bayyana cewa a bisa wannan mataki, yanzu haka sun fara tantance makarantun masu zaman kansu da yawansu ya ninka na gwamnati.

''Har yanzu ba mu san adadin waɗannan makarantu ba, amma muna nan muna kan kirgawa da tantance yawan nasu,'' in ji shi.

Ya kuma ƙara da cewa ''muna so mu tantance don mu gane a cikinsu waɗanda na gaskiya da waɗanda ba na gakiya ba - akwai waɗanda za mu iya mayar musu da lasisinsu, amma muna son sai mun tantance su a kan ƙa'idar cancantar da ma'aikatar ilimi ta ƙasa ta shimfida''.

Kwamishina Abdullahi Gusau, ya kuma bayyana takaicinsa a kan cewa sai ka ga kawai mutum ya samu shaguna sun mayar da su makaranta, kana ya ɗauki waɗanda ba su iya kammala karatu a matsayin malaman makarantar.

''Ba zamu yarda iyayen yara na kashe kuɗinsu wajen biyan makaranta, amma ana basu ilimi wanda bai dace ba,'' in ji shi.

''Muna so mu tsaftace ilimi a jihar Zamfara, ƙoƙarin da muke yi shi ne don mu gyara harkar ilimi na makarantun gwamnati kuma mu sa ido kan na masu zaman kansu,'' in ji shi.

Kwamishinan ilimin ya kuma ci gaba da ƙarin haske a kan cewa, makarantu masu zaman kansu a jihar ta Zamfara sun ninka na gwamnati yawa, wanda a yanzu haka ma'aikatar ilimin ba ta da masaniyar yawan makarantun masu zaman kan su a jihar. sannan abin da gwamnati ke ƙoƙarin yi shi ne na ƙara hanyoyin za ta rika samun kuda shiga.

''Wadannan makarantu akasari ba su da rajista, gwamnati ba ta karuwa da su, sannan iyayen yara ba sa karuwa da su - domin ilimin da ake bai wa ƴaƴaansu ba shi da inganci.

"Za mu ci gaba da daukar wannan mataki har nan da zuwa watanni shida, amma idan mutum zai cika ƙa'idojin da ake buƙata ko da cikin mako guda ne, za mu iya bashi lasisi ya ci gaba da tafiyar da makarantarsa.

''Abin da muke buƙata a jihar Zamfara shi ne, ko da mutum ya samu kashi 50 bisa 100 na abin da ake buƙata, za mu iya mayar masa da lasisinsa ya ci gaba da tafiyar da makarantar''

Ƙa'idojin da gwamnatin Zamfara ta shimfida game da makarantun

  • Ana bukatar wuraren wasan yara kamar na ƙwallon ƙafa da ƙwallon kwando da makamantansu.
  • Lambu don shaƙatawar yara, ko wurin ajiye dabbobi
  • Wurin kiwon kifi inda za a rika koyar da yara kiwon kifi.
  • Ana kuma buƙatar asibitin sha-ka-tafi, don kula da lafiyar yaran, musamman ma saboda annobar korona ta addabi duniya.
  • Akwai buƙatar likita ko ma'aikaciyar jinya mai rajista don kula da bangaren asibitin
  • Ana buƙatar malaman da suka cancanta su koyar - kamar masu takardar shaidar karatun NCE.
  • Ana so a san yaran da aka ɗauka a makaranta ko malamai nawa ne ke koyar da su
  • Sannan shi kansa shugaban makarantar ya kasance yana da takardar shaidar karatun da aƙalla ba ta gaza digiri ba.